--
Da duminsa: FG ta tsayar da ranar bude makarantun sakandire a cikin watan Agusta

Da duminsa: FG ta tsayar da ranar bude makarantun sakandire a cikin watan Agusta



Gwamnatin tarayya (FG) ta sanar da cewa za a bude makarantun sakandire a fadin kasa domin bawa daliban da ke shekarar karshe damar zana jarrabawar kammala karatun sakandire (WASSCE).

A cikin wata sanarwa da ma'aikatar ilimi ta fitar a yau, Litinin, ta bayyana cewa za a bude makarantun ne daga ranar Talata, 4 ga watan Agusta, 2020.


 Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Ben Bem Goong, darektan yada labarai na ma'aikatar ilimi ta kasa.

A cewar sanarwar, an yanke shawarar bude makarantun ne bayan masu ruwa da tsaki a bangaren ilimi sun shafe lokaci mai tsawo suna tattaunawa a ranar Litinin. Daliban da ke aji shidda; watau shekarar karshe, da takwarorinsu da ke aji uku ne kawai zasu koma makaranta, a cewar sanarwar.

SOURCE: LEGIT.NG

TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Da duminsa: FG ta tsayar da ranar bude makarantun sakandire a cikin watan Agusta"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?