
Da duminsa: El-Rufai ya amince da yin sallar Idi a Kaduna, ya bada sharudda 2
Thursday, 23 July 2020
Comment
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, ya amince da yin sallar idin babbar sallah a fadin jihar.
Gwamnan ya sanar da hakan ne a tattaunawar da yayi da manyan gidajen rediyon jihar Kaduna wanda aka fara da karfe 8 na daren ranar Alhamis.
Ya ce sharadin yin sallar idin shine tabbatar da cewa an yi shi a fili sannan a kiyaye dokokin dakile yaduwar annobar korona. Gwamnan ya bukaci dukkan masallatan da su garzaya gida bayan kammala sallar idin. Bai amince da yin shagalin bikin sallar ba.
Kamar yadda yace, "Na amince da yin sallar Idi a fadin jihar Kaduna amma a fili kuma tare da kiyaye dokokin dakile yaduwar COVID-19.
"Ana bukatar jama'a da su koma gida bayan kammala sallar amma ba a amince da su yi wani bikin shagalin sallah ba wanda za a tara taro."
A jawabin mataimakiyar gwamnan jihar, Hajiya Hadiza Balarabe, ta yi kira ga mazauna jihar da su kasance 'yan kasa nagari.
Ta bukacesu da su rungumi zaman lafiya tare da bada himma wurin kiyaye kai. Saka takunkumin fuska, zaman gida, nesa-nesa da juna, tsaftar numfashi, wanke hannuwa da sabulu da ruwa, gujewa taron jama'a masu yawa da cin abinci mai lafiya zai taimaka.
SOURCE: LEGIT.NG
TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Da duminsa: El-Rufai ya amince da yin sallar Idi a Kaduna, ya bada sharudda 2"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?