--
Da dumi duminsa: 'Yan bindiga sun sace babban limamin rundunar 'yan sanda A Taraba

Da dumi duminsa: 'Yan bindiga sun sace babban limamin rundunar 'yan sanda A Taraba


‘Yan bindiga sun sace babban limamin rundunar 'yan sandan jihar Taraba, Mallam Mustapha Nuhu - Maharan da za su kai 10 sun tsinkayi gidan Malamin da ke kwatas din Nana Aisha a tsakar daren Lahadi tare da sace shi


A lokacin rubuta wannan rahoton, masu garkuwa da mutanen basu tuntubi iyalan dan sandan ba 'Yan bindiga sun sace babban limamin rundunar 'yan sandan jihar Taraba, Mallam Mustapha Nuhu. An yi garkuwa da babban dan sandan ne a daren ranar Lahadi, 12 ga watan Yuli,


jaridar Daily trust ta ruwaito. 'Yan bindigar da za su kai 10 sun tsinkayi gidan Malamin da ke kwatas din Nana Aisha a tsakar dare tare da sace shi. Malamin kuma babban dan sandan, na aiki da rundunar 'yan sandan jihar Taraba.

An gano cewa yayi wa'azi a kan yawaitar laifuka musamman garkuwa da mutane a jihar Taraba yayin hudubar ranar Juma'a. A lokacin rubuta wannan rahoton, masu garkuwa da mutanen basu tuntubi iyalan dan sandan ba.


Jaridar Daily Trust ta gano cewa, 'yan bindiga na ta kai hari a tsakiyar birnin Jalingo a cikin makonnin nan. An gano cewa, wuraren da abun ya shafa sun hada da kusa da gadar Donga, Baba Yau, Mile 6, Kona, Wuro Sambe, Sabongari da yankin firamare. An gano cewa mazaunan yankin ne cike da tsoro tare da fargabar masu garkuwa da mutanen.

Wani mazaunin kusa da fadar Donga mai suna Mathew Bulus, ya ce a yan kwanakin da suka gabata, wani ma'aikacin PHCN, Joseph Zaphania ya shiga hannun masu garkuwa da mutanen. Ya kara da cewar mutumin ya kuma mutu kwanaki kadan bayan da suka sako shi.

Ya ce 'yan bindigar sun kutsa yankin har sau uku a makon da ya gabaga amma sun yi yunkurin sace wani mai kudi,wanda hakan bai yuwu ba. An gano cewa, mutane da yawa a yankin sun shiga hannun 'yan bindigar amma an sako su bayan biyan kudin fansa.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Taraba, DSP David Misal, ya ce bashi da bayanin aukuwar lamarin. "Bani da bayanin nan a halin yanzu. Ku bani lokaci," DSP Misal yace.


SOURCE: legit.ng

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Da dumi duminsa: 'Yan bindiga sun sace babban limamin rundunar 'yan sanda A Taraba"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?