--
Da dumi duminsa: Daliban Najeriya ba za su rubuta WAEC ba a 2020 – FG

Da dumi duminsa: Daliban Najeriya ba za su rubuta WAEC ba a 2020 – FG



MINISTAN ILIMI ADAMU ADAMU 

Ɗaliban Najeriya da ke ajin karshe a makarantun sakandare ta gwamnatin tarayya ba za su rubuta jarrabawar kammala sakandare ta WAEC ba a bana a cewar gwamnatin tarayya. Ministan Ilimi, Mallam Adamu Adamu ne ya bayyana wa manema labarai hakan a ranar Laraba bayan kammala taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya, FEC.

Ya kuma kara da cewa har yanzu ba a tsayar da ranar da za a bude makarantun ba a kasar kamar yadda The Nation ta ruwaito. Adamu ya kuma bukaci gwamnatocin jihohi da ke shirin bude makarantu su hakura su canja shawara saboda annobar korona.

"Ina kira ga gwamnatocin jihohi da suka amince za su bude makarantu su sake shawara saboda halin da muke ciki na annobar COVID-19. Ina ganin akwai hatsari cikin yin hakan. Mu kare yaran mu," in ji shi.

Ya ce dukkan makarantun da ke karkashin gwamnatin tarayya za su cigaba da kasancewa a rufe har sai an tabbatar an ci galaba a kan cutar korona.

Ministan ya yi kira ga hukumar shirya jarrabawar ta Afirka ta Yamma, WAEC, da gwamnatocin jihohi su canja shawarar su ta bude makarantu don yin jarrabawa. A cewar Adamu, Hukumar WAEC ba ta da ikon fada wa makarantu lokacin da za su bude.

Ya ce ya gwammace daliban Najeriya su rasa shekarar karatu daya a maimakon jefa rayuwarsu cikin hatsari. Har wa yau, Ministan ya bayyana cewa za a yi wa dakunan kwanan daliban Kwallejin Fasaha ta Kaduna, Kadpoly, gyara. Ya ce wani mai saka hannun jari ne ya bayar da kudi N774,264,000 don yin gyaran. Ya tabbatar wa daliban kwallejin cewa gyaran ba zai saka ayi musu karin kudin dakunan kwanan ba.


SOURCE: LEGIT.NG



KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Da dumi duminsa: Daliban Najeriya ba za su rubuta WAEC ba a 2020 – FG "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?