
Ciki da reno: Me ke sa mata masu ciki ƙwalama?
Thursday, 23 July 2020
Comment
![]() |
Ba kowace mace ce ke fuskantar irin wannan ƙwalama ta masu ciki |
Mun sha jin labaran mata masu ciki wadanda ba abin da suke so sai ayis kirim da sauran kayan ƙwalam, inda suke aiken mazajensu har da tsakar dare don sayo musu tsire ko balangu ka gasasshiyar kaza ko agwaluma ko goruba ko yalo, ko kuma su ce ba abin da suke so sai cakulat, kuma ita din ma ta musamman.
Mai yiwuwa mu ma mun sha fama da irin wannan yanayin da kanmu.
An sha yada cewa ƙwalamar masu ciki na samo asali ne daga bukatar kayan gina jiki daga jikin mace ko ɗan tayinta, kuma akwai wani abu na ban mamaki da yake fito da ainihin bukatar jikinsu.
Sai dai hakan a wasu lokutan abu ne mai wahala.
Rainon cikin dan tayi lamari ne mai daukar lokaci da gajiyawar da sanya rashin sukuni, kuma wannan ne dalilin da ya sa suke jin duk duniya ba abin da suke so sai kayan ƙwalama.
Kazalika idan aka duba binciken kimiyya kan lamari, wasu abubuwa na ban mamaki da al'ajabi suna bijirowa.
![]() |
Matan Japan sun fi kwadayin shinkafa idan suna da ciki |
Kwaɗayin shinkafa
Masu bincike sun gano cewa ba kowace mace ce take tsintar kanta cikin yanayin ƙwalama ba,
Salon yadda mata masu fama da laulayi ke bayyana yadda suke ji a kasashen Amurka da Burtaniya ya bambanta da na matan da ke wasu kasashen.
Alal misali a Japan, idan aka ba da rahoton ƙwalama, yawanci abincin da mata suka fi kwadayi shi ne shinkafa.
Bincike ya ci gaba da duba ko ire-irien abincin da ake ƙwalamarsu suna taimaka wa wajen samar da kayayyakin gina jiki, amma sakamakon binciken bai gano hakan ba.
![]() | |||
Wasu matan kuma sun fi kwadayin cakulat |
Gwaji a kan cakulat
A takaice ma, matan da suka fi yin ƙwalama da ciki sun fi narka ƙiba wanda hakan barazana ce ga lafiyarsu, al'amarin da ke iya jawo musu tarnaki lokacin haihuwa.
Hakan ba ya nufin cewa matan da ke ƙwalama lokacin laulauyin ciki da gangan suke yi ba, sai dai kawai ƙwalamar da kan faru ne ba ta dalilin bukatar wani sindari ba.
![]() |
Masana sun gani cewa zuciya ce take raya kwalama fiye da bukatar jiki |
Duba kan dalilin da ya sa mutane gaba daya ke kwadayin abinci na iya fito da ma'anar wadannan bayanai fili, a cewar Julia Hormes, wata farfesa a Jami'ar New York Ta Amurka, wacce ta karanci fannin ƙwalama a al'ummomi daban-daban.
Alal misali, bincike ya nuna kusan kashi 50 cikin 100 na matan Amurka na kwadayin cakulat mako guda kafin su fara hailarsu, a cewar Hormes.
Masana kimiyya sun duba ko wannan kwadayin ya samo asali ne daga wasu sinadaran abinci da ke cikin cakulat da suke da muhimmanci a haila, ko kuma yana faruwa ne sakamakon sauyin kwayoyin halittar jiki dake sauya wa.
A wani bincike da aka gudanar, wani masanin halayyar dan adam ya umarci mata su bude wani akwati da aka ba su su kuma ci abin da ke ciki, daga lokacin sai suka fara kwalamar abin.
Wasu akwatunan sun kunshi cakulat mai madara (da ke kunshe da dukkan sinadaran cakulat da ke narkewa a baki idan ana ci.)
![]() |
Idan kika sa a ranaki cewa ba za a taba barinki ki ci wani na'uin abinci ba - to zai yi wuya ki iya kau da kai idan kika same shi |
Ko juna biyu 'wani abu ne na daban'?
Bai kamata a dinga kyarar masu ciki a lokacin da suke wannan yanayin na laulayi ba.
"Wasu matan kuma kan yi dabara su mayar da wannan lokaci na cin wasu abubuwa da watakila tuni aka hana su cin su,'' a cewar Hormes.
Hormes ta ba da shawarar cewa idan kina ƙwalamar cakulat, to ku ci mai kyau madaidaiciya a kowace rana, ku ci gaba da rayuwarku - hakan zai iya taimaka wa wajen rage kwadayinta.
Hanya daya ta yin hakan ita ce ta kawar da hankalinsu - akwai bincike da dama da aka yi amfani da abin kallo ko kamshi.
![]() |
Idan kina kwalamar wani abu, to zai fi kyau ki samu inagantacce kuma ki ci sannu-sannu |
Duba yanayin tunaninsu
Wata hanyar ita ce a duba yadda suke tunani domin sanin irin bukatar tasu.
Idan ana maganar kwalamar masu ciki, zai iya samun karuwar dalilai na al'ada: ciki yana zuwa da tsarabe-tsarabe, sannan zai yi wuya a shiga cikin yanayin ba tare da naiman taimako ba.
Wani bincike da aka yi ga wasu mata a wani kauyen Tanzaniya da ya nuna cewa mata masu ciki suna ƙwalamar kifi fa hatsi da kayan marmari da ganyayyaki ya lura da cewa samar da abincin da suke bukata wani nuna goyon baya ne gare su daga mazansu da kuma iyalensu.
Tabbas, kawo soyayyiyar kaza da karfe dayan dare daga mutumin da aka nemi ya kawo alawa, wani tabbaci ne na cewa wannan mutum yana ba wa mai ƙwalama kulawa.
Yayin da soyayyun fikafikan kaza da aka soya da fulawa suke da daraja a kan kansu, mutumin da ya kawo miki su ya nuna cewa yana matukar mutunta ki.
SOURCE: BBCHAUSA
TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Ciki da reno: Me ke sa mata masu ciki ƙwalama?"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?