
Boka da mutane sun kashe tsohuwa mai shekara 90 da duka kan zargin maita
Monday, 27 July 2020
Comment
Bokan ya zargi tsohuwar mai suna Akua Denteh da maita inda daga nan suka azabtar da ita na tsawon sa'o'i har ta rasa ranta.
Wani bidiyo da ya yadu kamar wutar daji ya nuna yadda mutane suka zagaye tsohuwar suka dinga dukanta da itatuwa a kanta tare da zane ta,yayin da take zaune a kasa har sai da ta fita hayyacinta, sannan daga bisani ta mutu.
Lamarin ya faru ne a Kafaba da ke yankin Salaga a ranar Alhamis din da ta wuce.
Rahotanni sun ce mutane sun dauki matar suka kai ta gidan bokan.
'Yan sanda a Kafaba sun dauki gawar matar suka kai mutuware a asibitin koyarwa na Tamale don yin gwaji.
SOURCE: BBCHAUSA
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Boka da mutane sun kashe tsohuwa mai shekara 90 da duka kan zargin maita"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?