--
Bidiyon da saurayi ya tsugunna wa budurwa don neman aurenta a Kano ya ta da ƙura

Bidiyon da saurayi ya tsugunna wa budurwa don neman aurenta a Kano ya ta da ƙura




Wani bidiyo da ke nuna yadda wani saurayi ya tsuguna a gaban budurwarsa tare da sanya mata zobe a hannunta don neman yardarta a jihar Kano ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin jama'a.

Mutane da dama sun yi ta mayar da martani a jihar da kuma a shafukan sada zumunta inda da dama ke cewa abin da matasan suka yi ya kauce wa tsarin neman aure a Musulunce.

Sun ce masoyan sun kwaikwayi al'adar Turawa maimakon su bi hanyoyin da addinin Musulunci da al'adar Bahaushe suka tanadar wajen neman aure.

Hukumar Hizbah ta jihar Kano ta ce za ta mayar da martani kan bidiyon a ranar Laraba.


Ga dai wasu daga cikin abubuwan da mutane suka dinga cewa a kan bidiyon.



 Ya ake baiko a addinin Musulunci?

Malam Dauda Ayuba limamin masallaci ne a Abuja ya kuma shaida wa BBC cewa abin da matashin dan jihar Kano ya aikata ya sabawa koyarwar addini Musulunci.

"A Musulunci idan ka ga yarinya kana so, abu na farko da zaka yi shine tura iyaye ko manyan ka su nemi izini daga iyayyenta. Daga nan, sai su ba ka izini ku gana da yarinya.

"Sannan idan kun fahimci juna da yarinya iyayyenka zaka sake turawa su nema maka aurenta.

"Don haka batun durkusawa ko bada zobe da sunan ta amince ka aureta ba tsarin addinin mu ko koyarwa addini ba ne".

SOURCE:BBCHAUSA

TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Bidiyon da saurayi ya tsugunna wa budurwa don neman aurenta a Kano ya ta da ƙura"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?