Bidiyo: Yadda wani kare ya daukewa wani makaho itace daga kan hanya domin ya samu ya wuce
Sunday, 12 July 2020
Comment
Kare dai ance shine babban abokin mutum. Yana nuna soyayya ga mutum ba tare da neman wani abu ba.
Wani kare mai hankali ya bawa mutane da yawa mamaki bayan ya taimaki wani makaho ya dauke masa wani itace dake kan hanyar shi.
Kwamishinan ‘yan sanda daga birnin Pune, ya sanya mutane da yawa hawaye, bayan ya wallafa bidiyon wannan kare da yayi wannan abu na gwaninta, ba tare da ya damu da wanda yake kallon shi ba.
Humanity— CP Pune City (@CPPuneCity) July 4, 2020
pic.twitter.com/cjXdfpa8zi
Wannan kare dai yana tafiya da wata budurwa ne, wacce ake kyautata zaton cewa karen nata ne, da farko dai karen bai damu ba, har sai da yaga makahon yana tahowa hanyar da suke bi.
Makahon yana bin hanyar shi yana tafiya a hankali tare da dan sandan shi, bai san cewa a gabanshi akwai wannan ice da idan har ya taka zai kada shi ba.
Cikin ikon Allah, sai Allah ya kawo wannan kare tare da mai shi za su wuce, inda ya gano wannan icen a gabanshi, cikin gaggawa ya juya yaje ya dauke itacen daga wajen, ya juya ya cigaba da bin budurwar ba tare da ya damu da wanda ke kallon shi ba.
Budurwar ta juya ta kalli lokacin da wannan kare nata yake wannan abu na bajinta, wanda ya ceto ran mutumin da bai san da shi ba a duniya.
SOURCE: PRESSLIVES.COM
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Bidiyo: Yadda wani kare ya daukewa wani makaho itace daga kan hanya domin ya samu ya wuce"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?