
Bidiyo: Dan shekara 95 da ya ce bai taba aske gashin kan shi ba, mutane sun dauke shi abin bauta
Thursday, 16 July 2020
Comment
Wani mutumi dan shekara 95 daga kasar Indiya jihar Karnataka, ya bayyana cewa bai taba aske gashin kanshi ba, wanda a yanzu haka yayi tsawo sosai da ya sanya dole ake nade mishi shi a dunkule mishi a kan shi.
A lokacin da aka hana zirga-zirga, mutane da dama sun damu saboda babu damar fita suyi aski, sai gashi shi kuma wannan bawan Allah ya bayyana cewa ya shafe kusan karni daya ba tare da ya taba yin aski ba.
Mutumin mai suna Doddapalliah, mutane da dama a garinsu na Molakalmuru, sun dauke shi a matsayin abin bauta, inda suke nade mishi gashin kan nashi a koda yaushe saboda ya samu damar yin tafiya kamar kowa.
A dan gajeren bidiyon, an nuno Doddapalliah yana nishi cikin jin ciwo yayin da mutane suke kokarin nade mishi wannan gashi nashi a kanshi.
Gashi dai yayi kamar an shafe lokaci mai tsawo ba tare da an wanke shi ba, ganin yadda ya nade waje daya.
Doddapalliah ba shine mutum na farko da aka fara bayyanawa da ya tara irin wannan gashin ba, akwai wani shi ma mai suna Sakal Dev Tuddu, shi ma daga kasar Indiya, wanda bai yanke gashin kanshi ba na tsawon shekara arba’in.
SOURCE: PRESSLIVES.COM
TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Bidiyo: Dan shekara 95 da ya ce bai taba aske gashin kan shi ba, mutane sun dauke shi abin bauta"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?