
Bidiyo: Budurwa ta kone motar saurayinta bayan ta kama shi da wata a otel
Friday, 24 July 2020
Comment
Wata budurwa mai tsananin kishi ta kusa kashe kanta bayan ta sanyawa motar saurayinta wuta da ya ajiye a cikin wani otel.
Budurwar dai da ta aikata wannan aika-aika an cafke ta tana hannun ‘yan sanda.
Bidiyon da yake ta yawo a shafukan sadarwa, ya nuna matar sanye da wani wando ruwan toka da bakar tana watsa fetur a cikin motar. A lokacin da ta kunna wuta a cikin motar, sai tayi bindiga, inda har ta jefota kasa. Cikin gaggawa ta tashi ta ruga a yayin da motar take ci da wuta.
A rahoton da NBC ta bayar, matar da ta aikata wannan abu sunanta Kelly S. Hayes mai shekaru 34 da ta fito daga Wisconsin.
Jami’an ‘yan sanda sun bayyana cewa wani shaida ya bayyana musu cewa matar ta fasa gilashin motar da wani itace kafin ta watsa fetur din a cikin motar.
Matar dai an cafke ta da laifin ta’addanci da kuma bata kayan mutumin babu gaira babu dalili.
‘Yan sandan sunce matar tana soyayya da mutumin da ya ajiye motar a wajen, sai rikici ya hado su bayan ta iske shi da wata a otel din.
SOURCE: PRESSLIVES.COM
TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Bidiyo: Budurwa ta kone motar saurayinta bayan ta kama shi da wata a otel"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?