
Balarabiya ‘yar shekara 8 da aka daurawa aure ta mutu a daren farko, bayan angon ya kwanta da ita ta karfin tsiya
Wednesday, 22 July 2020
Comment
Idan ana magana game da yara mata kanana, a wasu kasashen Musulman na duniya ba a duba shekaru a wasu abubuwan. Shekaru suna da matukar muhimmanci, saboda bawai yana sanya yara suyi hankali bane kawai, yana taimakawa wajen samun daidaito a jikinsu da kaiwa minzalin balaga.
Wani lamari da ya faru mai ban tausayi da ya faru sakamakon watsi da aka yi da yanayi na shekaru ya jawo kace-nace. Labari ne na wata yarinyar ‘yar shekara 8 daga kasar Kuwait wacce aka aurar a kasar Yemen, ta mutu a darensu na farko da angonta, bayan yayi mata ila a lokacin saduwa da ita.
Yanzu dai kafin mu cigaba, mutane suyi tunani a matsayinsu na masu tunani, ba tare da hange a bangaren addini ko al’ada ba. Yarinya ‘yar shekara 8 wacce ko balaga bata yi ba, ita ce aka aurar ana so ta biyawa mijinta bukata a bangaren jima’i, shin wannan abu ne mai kyau kuwa?
Amaryar mai suna Rawan, an ruwaito cewa ta mutu bayan jini yayi ta fita daga gabanta, sakamakon gabanta da y samu matsala sanadiyyar saduwa da ita da mijinta yayi a daren su na farko.
Masu rajin kare hakkin dan adam a kasashen Yemen da Kuwait sun bukaci hukumomi da su dauki mummunan mataki akan wannan ango, wanda ya auri yarinyar, kuma ya sadu da ita duk da ya san cewa ba ta kai minzalin hakan ba.
Haka kuma sun bukaci hukumomi da su dauki mummunan mataki akan dangin yarinyar, wadanda suka aurar da ita a mataki na wannan shekarun, duk da sun san cewa bata kai mataki na saduwa da namiji ba.
An ruwaito cewa angon yarinyar ya ninka shekarunta kusan sau sau biyar ko sau shida. Hakan na nufin yana da kimanin shekaru 40 har da doriya.
Lamarin ya jawo kace-nace sosai a shafukan sadarwa, inda aka dinga zagin angon, sannan aka dinga yiwa yarinyar addu’a da kuma rokon bi mata hakki akan wannan zalunci da aka yi mata.
SOURCE: PRESSLIVE.COM
TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Balarabiya ‘yar shekara 8 da aka daurawa aure ta mutu a daren farko, bayan angon ya kwanta da ita ta karfin tsiya"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?