
Babbar Sallah: Duba Sharudan Sallar Idi a Masallatan Abuja
Tuesday, 28 July 2020
Comment
Minisatan babban birnin tarayya (FCT), Malam Muhammad Musa Bello, ya ce za a gudanar da Sallolin Idi ne a harabar ginannun Masallatai kadai domin dakile yaduwar cutar korona a Abuja.
Bello ya sanar da hakan yayin da ya ke gabatar da jawabi a gaban wakilan kungiyar limaman Masallatan Abuja wadanda suka gana da shi a ranar Talata. A cikin wani jawabi da Mista Tony Ogunleye, sakataren yada labaran minista Abuja, ya fitar ya ce wakilan kugiyar limaman a karkashin jagorancin, Dakta Tajudeen M. B Adigun, sun gana da ministan ne domin tattauna Sallar Idi.
A cewar Oguleye, ministan da malaman sun fahimci juna tare da amincewa da wasu tsare - tsaren gudanar da Idin bikin babbar Sallah. Jawabin ya kara da cewa minista Bello ya yi la'akari da rahoton hukumomin tsaro da na hukumar lafiya tare da kiyaye sharudan kwamitin shugaban kasa mai yaki da annobar korona (PTF) kafin yanke shawara a kan gudanar da sallar Idi a Abuja.
Ministan ya sanar da cewa ba za a gudanar da Sallah a filin Sallar Eidi na kasa da ke kan babban titin Umaru Musa Yar'adu a birnin Abuja ba.
An umarci jama'a su gudanar da Sallar Idi a harabar Masallatan da su ka fi kusa dasu. "Kar a wuce sa'a guda yayin Sallar, za a gudanar da Salloli ne a tsakanin karfe 8:00 zuwa karfe 10:00 na safe. "A cikin gida kadai aka yarda a gudanar da duk wasu shagulgulan bikin Sallah saboda har yanzu dokar rufe wuraren haduwar mutane domin shakatawa da nishadi ko motsa jiki ta na aiki,"
a cewarsa. Ministan ya bukaci shugabannin kungiyoyin Masallatai su kula da shige da ficen jama'a a wuraren bauta. Duk sauran dokoki da ka'idojin da hukumar kula da birnin Abuja (FCTA) ta rabawa wuraren ibada su na nan, su na aiki, kamar yadda sanarwar ta bayyana. A ranar 31 ga watan Yuli, 2020, ne Musulmai a Najeriya da sassan duniya za su fara gabatar da bukukuwan babbar Sallah.
SOURCE: LEGIT.NG
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Babbar Sallah: Duba Sharudan Sallar Idi a Masallatan Abuja "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?