--
Ba mu yadda ba>>PDP bangaren Inyamurai suka fada kan tsayar da dan takarar shugaban kasa dan Arewa

Ba mu yadda ba>>PDP bangaren Inyamurai suka fada kan tsayar da dan takarar shugaban kasa dan Arewa

PDP bangaren Kudu maso gabas sunce basu amince da rade-radin dake yawo cewa wai jam’iyyar zata tsayar da dan takara daga Arewa ba a zaben shekarar 2023.


Mataimakin shugaban jam’iyyar daga bangaren, Austine Umahi ne ya bayyana haka inda yake inkarin sanata Gabriel Suswan game da cewa PDP dan Arewa zata tsayar takarar shugaban kasa a shekarar 2023.

Yace basu san da wannan magana ba dan ba jam’iyyar ce ta zaune ta yanke wannan shawara ba. Ya kara da cewa, yana kira ga jam’iyyar data fito ta warware wannan matsalar da samun nutsuwa.

Yace bai kamata a yi watsi da bangarensu na Inyamurai ba a jam’iyyar lura da irin gudummawar da suka bada wajan ci gabanta.

SOURCE: HUTUDOLE.COM


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Ba mu yadda ba>>PDP bangaren Inyamurai suka fada kan tsayar da dan takarar shugaban kasa dan Arewa"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?