
Asiri ya tonu: An kama tsohuwar sarauniyar kyau da ta zama Malamar makaranta tana turawa dalibinta dan shekara 15 hotunanta tsirara
Thursday, 23 July 2020
Comment
An kama tsohuwar sarauniyar kyau, bayan iyayen wani yaro sun gano hotunanta tsirara a cikin wayarshi.
Tsohuwar sarauniyar kyau din wacce ta yi aure ta koma koyarwa a makaranta, an yanke mata hukuncin shekara biyu a gidan yari, saboda laifin turawa yaro dan shekara 15 hotunanta tsirara, rahoton ABC.
Matar mai suna Ramsey BethAnn Bearse, wacce ta lashe gasar sarauniyar kyau a shekarar 2014, an kama ta da laifin cin zarafin yaro a watan Disambar shekarar 2019, bayan ta bayyana cewa kuskurene, hotunan tayi niyyar turawa mijinta ne.
Tsohuwar malamar makarantar wacce aka kama a watan Disambar shekarar 2018, bayan iyayen yaron sun ga hotunanta a cikin wayar dan nasu, an yanke mata hukunci a ranar Talata bayan ta bayyana cewa sunyi musayar hotunan tsakaninta da dalibin a Snapchat tsakanin watan Agusta da Oktobar shekarar 2018.
Bearse mai shekaru 29 an kuma sake yanke mata hukuncin shekara 10 domin sanya ido a kanta, kuma dole tayi rijista a matsayin wacce ta ci zarafin yaro tsawon rayuwarta.
A ranar Talata Bearse ta ce tayi na’am da abinda tayi kuma ta dauki alhakin hakan.
Ta bayyanawa kotu cewa ta cigaba da turawa yaron hotunanta tsirara a duk lokacin da ya nemi hotunan saboda tana tsoron kada yayi fushi.
“Tunda nice babba kuma shi yaro ne, na dauki laifin, kuma na yadda da duk hukuncin da za a yanke mini,” cewar Bearse a watan Disambar shekarar da ta gabata.
Saboda wannan abu ya sanya Bearse ta rasa aikinta na koyarwa wacce ta shafe shekara 8 tana yi.
SOURCE: PRESSLIVES.COM
TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Asiri ya tonu: An kama tsohuwar sarauniyar kyau da ta zama Malamar makaranta tana turawa dalibinta dan shekara 15 hotunanta tsirara"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?