
An kammala ƙera motocin farko masu amfani da wutar lantarki a Najeriya
Thursday, 23 July 2020
Comment
Wani kamfani a Najeriya mai suna JET Motor Company ya kirkiro mota mai amfani da wutar lantarki da za ta yi tafiyar kilomita 300 da caji Kamfanin ya samu tallafin kudi na dala miliyan 9 (N3,487,500,000) daga kasar Kanada, tare da jaddada bukatar neman tallafin gwamnatin kasar nan.
Gabanin dora motar a kan hanya wajen tabbatar da ingancinta, kamfanin ya samu tallafin kudi na dala miliyan 9 (N3,487,500,000) daga wata cibiyar samar da ci gaba a Afrika ta kasar Kanada.
An bude kamfanin JET Motor a shekarar 2017, inda bayan shekaru biyu ya fara kera jerin motoci da ake kira JET Mover wanda ana iya sauya fasalin cikinsu gwargwadon ra'ayin mabukata.
Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, Otal din Dolce Hanoi Golden Lake da ke Vietnam ya bayyana a matsayin otal na farko a duniya da aka yi wa fenti da zinari. Ba a dade da bude otal din ba don masu ziyara.
An bayyana kayan alatun da ke cikinsa inda da yawa daga cikinsu aka kawata su da zinari. Daga cikin akwai kwamin wanka na zinari, masai na zinari da ababen cin abinci na zinari. Babban otal din na nan a kusa da tafkin Giang Vo a tsakiyar garin Hanoi, babban birnin Vietnam.
SOURCE: LEGIT.NG
TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "An kammala ƙera motocin farko masu amfani da wutar lantarki a Najeriya"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?