--
An kama wani mutumi ya yiwa diyar matarshi mai shekaru 9 fyade a jihar Adamawa

An kama wani mutumi ya yiwa diyar matarshi mai shekaru 9 fyade a jihar Adamawa


Jami’an hukumar ‘yan sanda a jihar Adamawa sun kama wani magidanci mai shekaru 39, mai suna Obiora Patrick, da laifin yiwa diyar matarshi mai shekaru 9 fyade.

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan sandan jihar, DSP Sulaiman Nguroje, ya fitar, ya ce tuni mai laifin ya amsa laifinsa, yayin da ake duba lafiyar yarinyar a asibiti.

Sanarwar ta roki al’umma da su bayar da hadin kai wajen yaki da masu fyade da laifuka makamantan haka, inda sanarwar tayi kira ga iyaye da su sanya ido akan ‘ya’yansu sosai.

“Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa tana sanar da al’umma cewa sakamakon yaki da take yi akan masu yiwa mata da yara fyade, rundunar a ranar 20/07/2020, ta kama wani mai suna Obora Patrick, mai shekaru 39 a wani gida mai lamba 46 dake kan hospital road, dake Jimeta Yola North, da laifin yiwa diyar matarshi mai shekaru 9 fyade,” cewar sanarwar.

“Rundunar na kira ga al’umma da su bayar da hadin kai wajen yaki da fyade ga mata da yara, sannan kuma tana bukatar iyaye da su sanya ido sosai akan ‘ya’yansu.”

‘Haka kuma sanarwar ta cigaba da kara tabbatar da kokarinta wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma, inda ta bukaci al’umma da su kai rahoto ofishinsu da sun ga wani abu na zargi a kusa da su,” cewar sanarwar.

Source: PRESSLIVES.COM

TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "An kama wani mutumi ya yiwa diyar matarshi mai shekaru 9 fyade a jihar Adamawa"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?