
An kama saurayi da budurwa suna lalata a cikin mota a kasar Saudiyya
Wednesday, 22 July 2020
Comment
Kamar yadda kowa ya sani kasar Saudiyya na da doka mai tsauri akan kowanne mutum dake zaune a kasar. Babban laifi ne ga masoya da basu yi aure ba su kebance a waje koda kuwa bainar jama’a ne.
Irin wannan soyayyar an haramta ta a kasar ta. Idan muka yi la’akari da wannan doka, zamu gane cewa kasar bata dauki irin wannan abubuwa da wasa ba. Hakan ya sanya aka kama wani saurayi da budurwar shi bayan an kama su sun kadaice a cikin mota.
An kama su duka da laifin tarayya ba tare da aure ba da kuma shan giya a cikin kasar. Haka kuma a wannan Lahadi din an sake kama wasu saurayi da budurwa da suka yi abinda bai kamata ba a bainar jama’a a kasar.
Hukumomin na kasar Saudiyya sun kama saurayi da budurwar suna sumbatar juna a bainar jama’a suna daukar bidiyo. Saurayin ya dauki bidiyon a daya daga cikin manyan hanyoyin Jazan sannan ya dora akan shafinsa na Snapchat, inda yayi rubutu kamar haka ya ce “Ina koya mata yadda ake tuki”, daga baya dai wannan bidiyo ya yadu sosai.
A bidiyon mutumin yana koyawa budurwar yadda ake tuki, haka kuma an nuno su suna sumbatar juna a kujerar gaba ta motar.
Yarima Mohammed bin Abdulaziz ne ya bayar da umarnin kama masoyan. Ya sanya hukumomin kasar da suyi gaggawar kama masoyan bisa laifin yada wannan bidiyo da kuma saba dokar kasar.
Wannan bidiyo dai yayi ta yawo a shafukan sadarwa na kasar Saudiyya. Babu shakka ya bawa mutane da yawa mamaki a kasar.
Wasu suna ta fatan a kama su a jefa a gidan yari domin su koyi darasi akan abinda suka yi. Wasu kuwa suna ganin babu wani abu a wannan bidiyo.
“Bamu san menene a tsakaninsu ba, mai yasa mutane suke kokarin dora musu laifi akan soyayyar da suke,” cewar wasu daga cikinsu.
SOURCE: PRESSLIVE.COM
TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "An kama saurayi da budurwa suna lalata a cikin mota a kasar Saudiyya"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?