
An kama matasa maza da mata 25 suna daukar fim din batsa
Wednesday, 22 July 2020
Comment
‘Yan sanda a kasar Kenya sun ruwaito cewa sun kama wasu matasa a daidai lokacin da suke daukar fim din batsa tare da wani mutumi mai suna Caled wanda aka bayyana cewa shine shugabansu.
A cewar wani wanda lamarin ya faru akan idonshi, an kama su a ranar Litinin, 20 ga watan Yuli, a wani gida dake Maraba Estate da yamma a daidai lokacin da suke daukar shirin fim din batsar.
“Ina sana’ata ta bola-bola, sai na gano cewa akwai wani abu da yake faruwa da ban gane masa ba, naga kwaroron roba da yawa an saka a cikin wata leda an daure, sannan kuma na jiyo surutu daga cikin gidan.
“Dana shiga gidan abin ya bani tsoro da mamaki, domin kuwa mata ne da maza suna iskanci tsirara, sannan kuma naga wani mutumi a tsaye yana daukar su bidiyo.
“Na fita naje na sanar da ‘yan sanda, cikin gaggawa suka garzaya wajen da lamarin ke faruwa suka iske su suna lalata, wasu da kwaroron roba wasu kuma babu,” cewar mutumin da lamarin ya faru kan idonshi.
Jami’in dan sanda na Kakamega, David Kabena, wanda aka bayyana cewa ya tabbatar da kama matasan, ya ce aikinsu ya tafi yadda ya kamata bayan sun samu rahoton daga wajen mutumin sun je sun iske matasan a daidai lokacin da suke kan daukar bidiyon batsar.
“Dukansu yara ne, kuma mun kama su a daidai lokacin da suke iskancin. Za mu yiwa mutumin (Caleb) hukunci, saboda shine yake shugabantarsu zuwa wannan aika-aika,” cewar shugaban ‘yan sandan.
SOURCE: PRESSLIVES.COM
TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "An kama matasa maza da mata 25 suna daukar fim din batsa"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?