--
An dauki mata aikin Masallacin Ka’aba da Masallacin Annabi dake Madina

An dauki mata aikin Masallacin Ka’aba da Masallacin Annabi dake Madina




Ma’aikatar harkokin addini dake kasar Saudiyya ta dauki mata aikin Masallacin Ka’aba dake Makkah da kuma Masallacin Annabi dake Madina.

Ma’aikatar ta ce daga wannan lokacin matan da bangaren su za su dinga gyara da shirya komai a cikin Masallatan, wadanda suka hada da manyan ayyuka da ma’aikatan Masallacin suka saba gabatarwa.

Matan da aka dauka aikin za su dinga kula da bangaren mata na cikin Masallacin. Ma’aikatar harkokin addinin Musulunci ta kasar za ta dinga taimaka musu wajen gabatar da ayyukansu a duk lokacin da suke bukata, don taimaka musu wajen gabatar da aikinsu yadda ya kamata.

Manyan ayyukan da matan za su dinga yi a cikin Masallatan sun hada da:

Taimakawa wajen tabbatar da anyi sallah kamar yaddad hukumomin lafiya suka gindaya.

Shirya bangaren mata a lokaci da kuma bayan sallah a Masallaci.

Taimakawa mata a cikin Masallaci wajen kula da wasu muhimman bukatunsu.



Wannan dai zai taimaka matuka wajen mata su dinga gabatar da ibadunsu a cikin Masallaci kamar yadda ya kamata. Haka kuma zai taimaka wajen tabbatar da lafiyar kowa da kowa.

Source: PRESSLIVES.COM

TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "An dauki mata aikin Masallacin Ka’aba da Masallacin Annabi dake Madina"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?