--
Amurka Ta Sake Ambaton Shirin Makamai Masu Linzamin Kasar Iran A Matsayin Barazana

Amurka Ta Sake Ambaton Shirin Makamai Masu Linzamin Kasar Iran A Matsayin Barazana



Amurka Ta Sake Ambaton Shirin Makamai Masu Linzamin Kasar Iran A Matsayin Barazana Hoto daga Hausatv Source: hausatv


Jami’in gwamnatin Amurka na musamman mai kula da al-amuran kasar Iran ya sake nanata cewa gwamnatin kasar tana iya kokarinta na ganin an tsawaita takunkuman saya da sayar da makamai ga kasar Iran kafin watan Octoba na wannan shekara ta 2020.

Brian Hook ya bayyana haka ne a jiya Jumma’a a lokacinda yake jawabi a wata Jami’a mai suna Handison a kasar ta Amurka.

Hook ya kara da cewa shirin makamai masu linzami na kasar Iran babbar barazana ce ga zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya don akwai yuyuwan Iran ta yi amfani da su a kan HKI.

A ranar 18 ga watan Octoba mai zuwa ne za’a dagewa kasar Iran takunkuman saya da sayar da makamai kamar yadda kudurin kwamitin tsaro na MDD mai lamaba 2231 ya amince.

Gwamnatin kasar Iran dai ta bayyana cewa idan kwamitin tsaro ya kuskara ya tsawaita wadannan takunkuman to Iran za ta maida martani mai banmamaki.

SOURCE: HAUSATV.COM


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Amurka Ta Sake Ambaton Shirin Makamai Masu Linzamin Kasar Iran A Matsayin Barazana"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?