--
Amurka ta saɓa ka'ida wajen kashe Soleimani - Majalisar Ɗinkin Duniya

Amurka ta saɓa ka'ida wajen kashe Soleimani - Majalisar Ɗinkin Duniya



Sakamakon bincike da wakiliyar musamman ta Majalisar Dinkin Duniya kan kisan azarɓaɓi ta gudanar, ta bayyana cewa Amurka ta saɓa dokar ƙasashen duniya wajen kai harin da ya yi sanadin mutuwar babban janar din sojin Iran Qassem Soleimani.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta yi kakkausar suka game da sakamakon rahoton wanda ta kira 'Tarin shirme'.

A watan Janairu ne Amurka ta kashe Janar Qasem Soleimani tare da ƙarin mutum tara, ta hanyar kai hari ta sama kusa da filin jirgin sama na birnin Bagadaza da ke Iraqi.
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres

Sakamakon bincike na majalisar dinkin duniya ya ce Amurka ta gaza samar da isassun hujjoji da za su kare ikirarinta na cewa Janar din na kokarin kai hare-hare ga wasu ƙasashe ƙawayenta.

Wata mai magana da yawun ma'aikatar wajen Amurkan Morgan Ortagus, ta bayyana Janar Qaseim Solaimani a matsayin daya daga cikin rikakkun 'yan ta'adda a duniya, tana zargin mai binciken da boye hakan.

Ranar Alhamis ne ake sa ran Agnes Callamard za ta gabatar da sakamakon rahotonta, a gaban hukumar kare hakkin dan'adam ta majalisar dinkin duniya.



Wane ne Janar Qasem Soleimani?

Daga 1998, Manjo Janar Qasem Soleimani ya jagoranci dakarun Quds na rundunar juyin juya halin Iran wadda ke aiki a kasashen ketare cikin sirri.

Iran ta yaba da rawar da dakarun Quds suka taka a yakin Syria inda ta zamo mai bayar da shawara ga dakarun Shugaba Bashar al-Assad da kuma dubban masu rike da makami 'yan shi'a da ke mara musu baya.

A kuma Iraki, rundunar ta Quds ta mara wa wasu dakaru na musamman da ke da goyon bayan 'yan shi'a wajen yaki da kungiyar IS.
MANJOR GENERAL QASEEM SOLEIMANI

Janar din shi ne babban mai tsara dabaru na Iran a kan Iraki, inda ake kallonsa a matsayin babban mai tsara hare-hare da ayyukan kungiyoyin mayakan sa kai da Iran ke mara wa baya a Syria da Lebanon.

Kasashen Larabawa na daukarsa a matsayin wani shu'umi da ke iya bayyana a ko'ina kuma a ko da yaushe.

Amurka ta hallaka shi, a wani harin sama da sojojinta suka kai kan filin jirgin sama na Bagadaza, a Iraki, saboda zargin cewa yana shirin kai hare-hare ga wasu kawayen ta.


SOURCE: BBCHAUSA



KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Amurka ta saɓa ka'ida wajen kashe Soleimani - Majalisar Ɗinkin Duniya"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?