--
Amarya ta sace ‘yar da ta haifa don ta dorawa kishiyarta laifi a Katsina

Amarya ta sace ‘yar da ta haifa don ta dorawa kishiyarta laifi a Katsina




Jami’an ‘yan sanda a jihar Katsina sun kama wata mata ‘yar shekara 22 mai suna Fatima Bashir, da laifin sace ‘yar da ta haifa don ta dorawa kishiyarta da mijinta ya saki laifi.

Fatima ta aika da sakon waya, inda ta bukaci a bata naira miliyan biyu a matsayin kudin fansa.


Fatima wacce tayi kokarin dora laifin sace diyartan akan tsohuwar matar mijinta, ta bayyanawa ‘yan sanda cewa akwai lokacin da kishiyartan ta nemi daukar fansa akan mutuwar ‘yarta da ta mutu a hannunta.

Ta ajiye kayan sawa da takalman diyartan a gidan kishiyartan duka don ta dorawa kishiyar laifi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Gambo Isah, ya ce: “A ranar 5 ga watan Yuli da misalin karfe 8 na safe, matar ta kawo karar ofishin ‘yan sanda na Mashi cewa an sace diyarta, kuma ta nuna cewa kishiyarta ce ta sace ta.

“Bayan bincike, matar ta bayyana cewa ita ce ta aikawa da mijinta sakon waya akan neman kudin fansa, inda ta nemi ya bayar da naira miliyan biyu ko kuma ya rasa diyarshi.”

Fatima ta dauki diyarta daga gidansu dake Mashi ta kai ta Kano, inda ta boye ta da taimakon ‘yar aikinta mai suna Faiza. An kama ta a lokacin da take kokarin ajiye diyartan a kusa da gidan mahaifiyar kishiyartan dake Dutsi.

SOURCE: PRESSLIVES.COM

TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Amarya ta sace ‘yar da ta haifa don ta dorawa kishiyarta laifi a Katsina"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?