
Akwai sauran tsalle: Gwamnatin tarayya ta sake shawara kan bude makarantu
Friday, 3 July 2020
Comment
Shugaban kwamitin gudanarwa na yaki da cutar COVID-19, kuma sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Boss Mustapha, shine ya bayyana haka a jiya Alhamis 2 ga watan Yuli, yayin da yake bayani game da komawa makarantun, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.
Da yake magana a wajen taron kwamitin a Abuja, shugaban ya ce iya daliban da za su yi jarrabawa kawai za a bari su koma makaranta domin maimaita karatun da suka yi a baya kafin jarrabawar.
“Saboda gujewa shakku, ba za a bude makarantu ba. Iya daliban da suke bukatar rubuta jarrabawa kawai za a bari su koma su maimaita darasin da suka yi a baya kafin jarrabawar,” ya ce.
“Kamar yadda muka sanar daku, ma’aikatar ilimi ta kasa za ta yi shawara da masu ruwa da tsaki domin bayar da ka’idoji na komawa makaranta baki daya.”
Ya bukaci iyaye da su tabbatar da ‘ya’yansu suna amfani da fasahar zamani ta karatu a yanar gizo da aka kawo.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Akwai sauran tsalle: Gwamnatin tarayya ta sake shawara kan bude makarantu"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?