--
Akwai sabuwar annobar da ke jiran Nigeria - Gwamnatin tarayya

Akwai sabuwar annobar da ke jiran Nigeria - Gwamnatin tarayya

Akwai sabuwar annobar da ke jiran Nigeria - Gwamnatin tarayya Source: Twitter Source: Twitter 


Mr Boss Mustapha Ya ce Nigeria zata fuskanci wata babbar annoba ma damar aka gaza bunkasa fannin kiwon lafiyar kasar - Ya ce cutar Covid-19 ta fito da gazawar fannin kiwon lafiya, da gazawar gwamnati, da gazawa ta fuskar tsaro

Babban bankin Nigeria ya ce a halin yanzu, akwai ayyuka 20 da aka kashewa akalla N26.278bn karkashin shirin tallafi ga fannin lafiya na N100bn Gwamnatin tarayya ta ce Nigeria zata fuskanci wata babbar annoba ma damar ta kasa amfani da yanayin da annobar COVID-19 wajen bunkasa fannin kiwon lafiya.

Sakataren gwamnatin tarayya (SGF) Mr Boss Mustapha ya bayyana hakan a lokacin kaddamar da hukumar kwararru (BoE) na shirin bincike da bunkasa kiwon lafiya (HSRDIS) a Abuja. A cewar sa: "Idan har muka tsallake wannan yanayin, to lallai zamu fuskanci wata annobar kuma ba zamu iya tsinana komai ba,

"Idan da ace mun bunkasa fannin kiwon lafiya a lokacin annobar Ebola, da bamu sha wahalar da muka sha a yanzu ba, tunda cibiyoyin gwajin COVID-19 biyu kadai garemu." Ya kara da cewa: "Idan da zaka zagaya kasar nan, zaka samu sama da cibiyoyin kiwon lafiya 10,000,

amma kalilan ne ke da kayan aiki, wasu ma ba a amfani da su." Ya roki mambobin kwamitin kwararrun da su yi bincike kan gine ginen gwamnati na kiwon lafiya banda bangaren aikin da aka dauke su.

Cutar COVID-19, a cewar sakataren gwamnatin tarayyar, "ta fito da gazawar fannin kiwon lafiya a kasar, da gazawar gwamnati, da gazawa ta fuskar tsaro, da matakan kariya a tsakanin al'umma." Ya yi gargadin cewa: "Zai zama abun kunya garemu idan har bamu yi amfani da wannan lokacin wajen kawo karshen matsalolin dake addabar kiwon lafiya da gine ginenmu ba." Gwamnan babban bankin Nigeria, Godwin Emefiele, ya ce:

"A halin yanzu, akwai ayyuka 20 da aka kashewa akalla N26.278bn karkashin shirin tallafi ga fannin lafiya na N100bn." Ya bayyana cewa "wasu daga cikin cibiyoyin da suka samu tallafin sun hada da asibitoci, cibiyoyin bincike da kuma kamfanonin sarrafa magunguna."

Sai dai, darakta sashen bunkasa kudi na CBN, Mr. Philip Yila Yusuf ya bayyana cewa CBN ta samu bukatu 27 daga masu bincike dake bukatar tallafin N67bn. Tallafin kudin zai taimaka masu wajen samar da rigafi, bunkasa karfin magunguna da samar da kayayyaki daban daban da zasu taimakawa Nigeria wajen magance matsalolin da ke addabar fannin kiwon lafiya.

SOURCE: LEGIT.NG

TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Akwai sabuwar annobar da ke jiran Nigeria - Gwamnatin tarayya "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?