--
Batun jarrabawar WAEC Ministan ilimi yayi qarin haske akan haka

Batun jarrabawar WAEC Ministan ilimi yayi qarin haske akan haka




Gwamnatin Najeriya ta fayyace maganar da tayi game da hukuncin hana makarantun sakandire na gwamnatin tarayya daga rubuta jarabawar WAEC a wannan shekara  Karamin ministan ilimi ya ce gwamnatin tarayya ba ta da hurumin yanke hukuncin hana makarantu masu zaman da na gwamnatin jihohi zana jarabawar a bana

Ana iya tuna cewa, a baya bayan nan ne gwamnatin ta sanar da cewa makarantun sakandire da ke karkashin kulawarta ba za su zana jarabawar WAEC ba bana Bayan sanarwar da gwamnatin tarayya ta yi na hana makarantun sakandire rubuta jarabawar WAEC a wannan shekara,

a yanzu ta fayyace ainihin abin da sanarwar ta kunsa. Gwamnatin ta sanar da cewa ba ta da ikon hana makarantu masu zaman kansu da na gwamnatocin jihohi zana jarabawar WAEC a bana. Gwamnatin ta ce dukkanin makarantun da ba sa karkashin gudanarwarta, ganin damar su ne su yanke nasu hukuncin na zana jarabawar a bana ko kuma sabanin haka.

Karamin minsistan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, shi ne ya yi wannan karin haske yayin zaman kwamitin fadar shugaban kasa mai yaki da cutar korona da aka gudanar a ranar Litinin cikin birnin Abuja. Idan ba a manta ba, a baya bayan nan ne ministan ilimi, Mallam Adamu Adamu, ya sanar da:

cewa daliban makarantun sakandire na gwamnatin tarayya ba za su rubuta jarabawar WAEC ba a bana. Sanarwar da Mallam Adamu ya fitar, ya ce makarantun sikandire na gwamnatin tarayya ba za su rubuta jarrabawar ba ta bana wadda aka kayyade za a gudanar daga ranar 5 ga watan Agusta zuwa 5 ga Satumba.

SOURCE: LEGIT.NG

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657


0 Response to "Batun jarrabawar WAEC Ministan ilimi yayi qarin haske akan haka "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?