
Abin da ya sa na ke kwanciya da Agola – ‘Dan shekara 31 ya yi wa ‘Yan sanda bayani
Thursday, 23 July 2020
Comment
Wani mutumi mai shekara 31 mai suna Musa Abubakar da ake zargi da laifin fyade, ya yi wa ‘yan sanda bayanin abin da ya kai shi ga lalata da ‘diyar mai dakinsa. Da dakarun ‘yan sanda na reshen jihar Ribas su ka cafke shi, Musa Abubakar ya tabbatar da cewa ya yi wa karamar yarinyar da matarsa ta haifa fyade.
Abubakar ya shaidawa ‘yan sanda cewa yakan kwanta da wannan yarinya mai shekara tara a Duniya a duk lokacin da mahaifiyarta ta yi gardamar kwanciya da shi. Jaridar Vanguard ta ce wannan matashi ainihinsa mutumin jihar Jigawa ne wanda ya ke zaune a garin Rupokwu da ke karamar hukumar Obio Apor, jihar Ribas.
Jami’an tsaro sun gabatar da wanda ake tuhuma da laifin fyaden ne a ranar Laraba, 22 ga watan Yuli, 2020, ya kuma amsa ya yi laifin da ake zarginsa da shi. Mista Abubakar ya ce mai dakinsa ta aure ta kan guje masa, ta na korafin bai da kwazo a gado, don haka ya rika tarawa da wannan ‘yar yarinya da ke gidansa.
Da ta ke bayanin ta’adin da mijin mahaifiyarta ya yi mata, wannan yarinya ta ce Abubakar ya fara kai mata farmaki ne tun ta na da shekara hudu rak a Duniya. Yarinyar ta ce mutumin ya fara amfani da ita ne a wancan lokaci ya na jefa mata hannu a cikin al’aura, amma ta ji tsoron ta kai kara gaban mahaifiyarta wanda ya ke aure.
Ta ce a karon farko da ta koka cewa Abubakar ya na amfani da ita, tsohuwarta ta yi mata duka. A karshe yarinyar ta ce ta fasa kwai ne bayan uwarta ta yi alkawarin ba za ta doke ta ba. Ta ce: “Na fadawa uwata gaskiyar abin da ya faru.”
“Daga nan makwabta su ka duba ni, kafin a kai maganar gaban ‘yan sanda.” Inji wannan yarinya da ake zargin an yi lalata da ita. Kakakin ‘yan sanda na jihar Ribas, Nnamdi Omoni, ya tabbatar da wannan lamari. Omoni ya ce ‘Yan Sanda za su gurfanar da Abubakar da zarar an kammala bincike.
Source: Legit
TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Abin da ya sa na ke kwanciya da Agola – ‘Dan shekara 31 ya yi wa ‘Yan sanda bayani "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?