Zamfara: Karanta yanda aka tuɓe shugabannin ƙaramar hukuma 14 a Zamfara
Friday, 5 June 2020
Comment
Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta sauke shugabannin ƙaramar hukuma 14 bayan wata ganawar gaggawa sannan 'yan majalisar suka nemi Gwamna Bello Matawalle ya naɗa kantomomi.
Shugaban kwamitin yaɗa labarai na majalisar, Shamsudden Mafara ne ya sanar da hakan bayan kammala zaman a yau Juma'a yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai.
Shamsudden Mafara ya ce a cikin shawarwarin da suka bai wa gwamnan sun buƙaci a gudanar da zaɓe a ƙananan hukumin da abin ya shafa cikin wata uku masu zuwa.
Awani Lbarin na daban Kotun Ƙoli ta tabbatar da tuɓe rawanin Aminu Babba Ɗan'agundi
Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da matakin da marigayi Sarkin Kano da ke Najeriya, Alhaji Ado Bayero ya dauka na tube rawanin Aminu Babban Ɗan'agundi daga mukaminsa na Sarkin Dawaki Maituta kuma hakimin Gabasawa.
Da take tabbbatar da hukuncin, Mai shari`a Mary Odili, wacce ta jagoranci alkalan Kotun Kolin su biyar, ta ce matakin da marigayi Ado Bayero ya dauka yana kan ka'ida.
A shekara ta 2003 ne marigayi mai martaba Sarkin Kano Ado Bayero ya sauke Aminu Babba Dan`agundi daga mukamin nasa, bayan an zarge shi da nuna rashin da`a ga sarki, da aikata wasu laifuka da suka saba da dabi`un mai rike da mukami irin nasa.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Zamfara: Karanta yanda aka tuɓe shugabannin ƙaramar hukuma 14 a Zamfara"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?