--
Yanzu yanzu: Karin mutum 350 sun kamu da korona a Najeriya, jimilla 11516

Yanzu yanzu: Karin mutum 350 sun kamu da korona a Najeriya, jimilla 11516



ROHOTON: LEGIT.NG


Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa a Kasa (NCDC) ta ce annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 350 a fadin Najeriya. Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 11.43 na daren ranar Alhamis 4 ga Yuni na shekarar 2020.


A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa karin sabbin mutum 350 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka;

Lagos-102

Ogun-34

FCT-29

Borno-26

Kaduna-23

Rivers-21

Ebonyi-17

Kwara -16

Katsina-14

Edo-10

Delta-10

Kano-10

Bauchi-10

Bayelsa-9

Imo-8

Plateau-4

 Ondo-3

Nasarawa-2

Gombe-1

Oyo-1

Alkalluman da hukumar ta NCDC ta fitar a ranar Alhamis 4 ga Yuni 2020 ya nuna cewa jimillar wadanda suka kamu ta cutar ta korona a kasar 11516. An sallami mutum 3535 bayan an tabbatar da sun warke sarai,


a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 323. A wani rahoton, kun ji cewa 'yan sanda sun kama wani matashi, Ishaku mai shekaru 21 da haihuwa saboda kashe abokinsa, Zeloti ta hanyar daba masa wuka don rikici a kan budurwa.


Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a wani mashaya a garin Dass a ranar Juma'a 29 ga watan Mayu inda Ishaku ya caka wa Zeloti wuka har sau uku kan musun da suke yi a kan wanene ainihin saurayin yarinyar.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Bauchi, DSP Ahmed Wakili ya tabbatar da afkuwar lamarin kamar yadda LIB ta ruwaito.


Wakili ya ce an garzaya da Zeloti John zuwa babban asibitin garin Dass inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa. An birne shi a ranar 1 ga watan Yunin shekarar 2020.


Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan ya ce an kama wanda ake zargin kuma yana tsare yayinda ake cigaba da binciken gano musababbin mutuwar mammacin.



KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/






KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Yanzu yanzu: Karin mutum 350 sun kamu da korona a Najeriya, jimilla 11516"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?