
Yanzu-yanzu: An dawo da Adams Oshiomole Kujerarsa
Saturday, 20 June 2020
Comment
Legit ta ruwaito cewa an dakatad da kwamred Oshiomole ne daga jam'iyyar a watan Nuwamba 2019 bayan rikicin ya kaure tsakaninsa da Godwin Obaseki, gwamnan jihar Edo. Bayan haka wata kotu dake zamanta a Abuja ta dakatad da shi daga kujerar shugaba inda tace ba zai yiwu ya cigaba da zama shugaban uwar jam'iyyar ba tun da an koreshi daga jam'iyyar a gundumarsa. A ranar 4 ga watan Maris ne kotun ta amince da bukatar wasu mambobin APC shida na jihar Edo wajen dakatar da Oshiomhole.
A ranar 16 ga Yuni kuwa, Kotun daukaka kara da ke Abuja ta jaddada dakatar da Adams Oshiomhole a matsayin shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC). Alkalan kotun da suka samu jagorancin shugaban alkalan kotun daukaka kara, Mai shari'a Monica Dongban-Mensem sun yanke hukuncin cewa daukaka karar Oshiomhole bata da tushe. Hakan ya faru ne a ranar da Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya fita daga jam'iyyar APC bayan ganawarsa da Farfesa Ibrahim Gambari, shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Daga ranar aka shika rikici a jam'iyyar inda mutane biyu suka dane kujerar Oshiomole matsayin shugaban jam'iyyar na riko. Yayinda kwamitin gudanarwa NWC ta alanta mataimakin shugaban jam'iyyar (yankin kudu), Abiola Ajimobi, matsayin mukaddashin shugaba, mataimakin sakataren jam'iyyar, Victor Giadom, ya ce shine sahihin mukaddashin shugaban.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Yanzu-yanzu: An dawo da Adams Oshiomole Kujerarsa"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?