--
Yanzu-Yanzu: Buhari ya amince a bude Masallatai, majami'u da kasuwanni a fadin tarayya

Yanzu-Yanzu: Buhari ya amince a bude Masallatai, majami'u da kasuwanni a fadin tarayya



ROHOTON: LEGIT.NG

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da shawarar kwamitin kar ta kwanan fadar shugaban kasa kan cutar COVID-19 PTF na sassauta dokokin da aka kafa domin takaita yaduwar cutar. Shugaban kwamitin wanda shine sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya sanar da cewa an sun gana da shugaba Buhari kuma sun bashi shawara kan matakin da za'a dauka gaba.

Bayan ganawar, Shugaban kasa ya amince da bude wuraren Ibada (Masallatai da Majami'u kadai) da kasuwanni a fadin tarayya amma da sharadin za a bi dokokin da hukumar NCDC ta gindaya.

Yace: "PTF ta mika shawarinta kuma shugaba Muhammadu Buhari ya rattafa hannu a aiwatar da su cikin makonni hudu masu zuwa fari daga ranar 2 zuwa 29 ga watan Yuni, 2020." "An sassauta dokar hana taruwa a wuraren Ibada bisa ga sharudan da PTF ta gindaya da kuma yardar gwamnatocin jihohi."

"Za'a amince a rika shiga kasuwanni da wuraren tattalin arziki amma da lura saboda takaita yaduwar." cutar,





  KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Yanzu-Yanzu: Buhari ya amince a bude Masallatai, majami'u da kasuwanni a fadin tarayya"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?