--
Yanzu-yanzu: Bayan musayar wuta, dakarun soji sun fatattaki 'yan Boko Haram

Yanzu-yanzu: Bayan musayar wuta, dakarun soji sun fatattaki 'yan Boko Haram



ROHOTON: LEGIT.NG

Yan bindigar da ake zargin mayakan ta'addancin Boko Haram ne a halin yanzu sun kai hari kananan hukumomi biyu na jihar Borno a lokaci daya, majiyar jami'an tsaro ta sanar. Mayakan ta'addancin sun tsinkayi garin Monguno wurin karfe 11:30 inda suke ta harbe-harbe ta ko ina. 

Kamar yadda majiya daga jami'an tsaro ta tabbatar, ana musayar wuta tsakanin 'yan ta'addan da dakarun sojin Najeriya. Ma'aikacin NGO ya sanar da jaridar Daily Trust cewa harbe- harben bindiga da kararta ne yake ta tashi ta ko ina.

"A halin yanzu da muke magana, mayakan suna nan a Monguno, ana ta jin tashin karar bindiga. Dakarun soji na ragargazarsu. Ba mu da kwanciyar hankali, ku yi mana addu'a," yace. Hakazalika, 'yan ta'adddan sun kai hari a wani kauye mai suna Usmanati Goni da ke karamar hukumar Nganzai a sa'o'in farko na ranar Asabar.

Kamar yadda wani mafarauci ya sanar, maharan sun bayyana wurin karfe 10 na safe inda suka fara harbin farar hula. Har a halin yanzu ba a san yawan jama'ar da aka kashe ba a yayin rubuta wannan rahoton.

Rundunar sojin Najeriya ta fatattaki mayakan ISWAP a garin Monguno da ke jihar Borno ta yankin arewa maso gabas din kasar nan. Jami'an tsaro da mayakan sun yi musayar wuta bayan da 'yan ta'addan suka kutsa garin a ranar Asabar tare da fara harbe-harbe. Dubban 'yan gudun hijira da ke garin sun fara tserewa don neman mafaka.

Channels TV ta gano cewa, mayakan sun kai hari garin Nganzai da Gubio a lokaci daya duk da ba a samu rashin rayuka ba. Harin ya zo ne bayan da annobar korona ke hauhawa a jihar Borno. A ranar Juma'a, an gano cewa mutum 42 sun sake kamuwasa cutar, kamar yadda hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya ta bayyana.

A halin yanzu, jihar Borno ce ke da mafi yawan masu cutar a yankin arewa maso gabas inda ta tabbatar da kamuwar mutum 423 da mutuwar mutum 26.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Yanzu-yanzu: Bayan musayar wuta, dakarun soji sun fatattaki 'yan Boko Haram"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?