
Wata Wakiliya A Majalisar Wakilan Amurka Musulma Ta Yi Allawadai Da Trump
Sunday, 21 June 2020
Comment
![]() |
Ilham Umar wakiliya a majalisar wakilan kasar Amurka |
Kamfanin dillancin labaran “Jawan” na kasar Iran ya nakalto Umar tana fadar haka a yau Lahadi, ta kuma kara da cewa shugaban kasar yana tsammani da sakonnnin da yake rubutawa a shafuffukansa na Twitter ne zai gudanar da harkokin kasar.
Ilhan Umar dai ita ce wakiliya musulma da aka fara zaba zuwa majalisar wakilan kasar ta AMurka. Kuma ta dade tana sukan yadda shugaban yake gudanar da harkokin tafiyar da kasar.
Ya zuwa yanzu dai cutar Korona ta kama mutane kimani 2,330,000 tun lokacin bullatar a kasar a cikin watan Maris da ya gabata, sannan mutane akalla 120, 000 daga cikinsu dun rasa rayukansu.
Har’ila yau kissan wani bakar fata a ranar 25 ga watan Mayun da ya gabata ya tunzura mutanen kasar ta Amurka fitowa zanga-zangar yin allawadai da tsarin wariya, sannan suna bukaci a kawo sauyi a wannan tsarin wanda ya dade yana cinye rayukan bakar fata a kasar.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Wata Wakiliya A Majalisar Wakilan Amurka Musulma Ta Yi Allawadai Da Trump"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?