--
WATA SABUWA: Na Biya Mata Kudin Zuwa Kasashen Dubai, Saudiyya, Ingila Da Chana, Don Haka A Biya Ni Dukkan Kudaden Da Na Kashe Mata, Cewar Tsohon Saurayin Amaryar Shugaban Kwastan, Hameed Ali

WATA SABUWA: Na Biya Mata Kudin Zuwa Kasashen Dubai, Saudiyya, Ingila Da Chana, Don Haka A Biya Ni Dukkan Kudaden Da Na Kashe Mata, Cewar Tsohon Saurayin Amaryar Shugaban Kwastan, Hameed Ali



Tsohon Saurayin Hajiya Zainab Abdullahi Yahaya, Amaryar shugaban hukumar Kwastan Hameed Ali ya nemi da ta dawo masa dukkan kudaden da ya kashe mata a lokacin da suke soyayya da suka hada da na tafiye-fiyen da ya biya mata zuwa Saudiyya, Dubai, UK da China.

Saurayin mai suna Zubairu Ɗalhatu Malami, ya bayyana cewa Zainab ta yaudareshi domin ta bayyana cewa babu wanda za ta aura in ba shi ba daga baya ta tsallake shi zuwa wani tsoho mai maiƙo.

Wani babban ɗan jarida mai zaman kansa George Omonya Daniel ya ruwaito cewa babu tabbacin ko Hameed Ali ya san da wannan batu, amma lallai tsohon saurayin ya ce ba zai bari hau ta haushi domin ba zai yi biyu babu ba.

Alhaji Zubairu ya nemi haƙinsa ne ta hanyar lauyansa, inda aka aika wa da tsohuwar budurwar da takarda bukatar biyan waɗannan kuɗaɗe.




A cikin takardar wadda ta bayyana a kafafen sadarwa, Zubairu Dalhatu Malami ya bukaci  ta biyashi jimillan kuɗi naira miliyan tara da dubu tamanin da ɗaya (N9,81,207,45m) tare da dawo masa da katin shaidar aiki a kamfaninsa da ya bata tare da kannenta.

Harwayau ya nemi ta dawo da wasu kayan sawa, kayan aikin kamfanin da kuma kwamfutocin kamfani dake hanunta da kannenta tare da maido da lambar mota mai dauke da sunan karamar hukumar Bichi dake gunta.

Lauyan ya yi barazanar cewa ƙin biyan kudaden tare da dawo da dukkan abinda aka bikata zai iya kaiwa ga daukar mataki a dokace bisa umarnin Alhaji Zubairu Malami.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "WATA SABUWA: Na Biya Mata Kudin Zuwa Kasashen Dubai, Saudiyya, Ingila Da Chana, Don Haka A Biya Ni Dukkan Kudaden Da Na Kashe Mata, Cewar Tsohon Saurayin Amaryar Shugaban Kwastan, Hameed Ali"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?