
Wanda ake zargi da bata jarirai a Jihar Nasarawa ya shiga hannun Dakarun NSCDC
Wednesday, 24 June 2020
Comment
![]() |
Yaro a hannun Dakarun NSCDC Hoto: Daily Trust Source: Twitter |
Idan ba ku manta ba a ranar 27 ga watan Mayu, aka samu labarin cewa an yi wa wata karamar yarinya mai suna Rukayya Aliyu fyade. Wannan jaririya ba ta wuce kwanaki 90 a Duniya ba. Rahotanni sun bayyana cewa an yi yunkurin yin irin wannan lalata da wata jaririya mai watanni biyu da haihuwa.
An kai wannan hari ne jim kadan bayan an yi lalata da Rukayya Aliyu. An fahimci a kan yi amfani da irin wadannan kananan yara ne wadanda ba su wuce watanni uku zuwa shida da zuwa Duniya ba. Daga nan kuma a jefar da su a kusa da wata makaranta.
![]() |
Yaro a hannun Dakarun NSCDC Hoto: Daily Trust Source: Twitter |
Babban jami’in NSCDC na jihar Nasarawa, Gidado Fari, ya ce za a gurfanar da Ahmadu Yaro a gaban kotu. Za a yi wannan ne da zarar an kammala binciken da ake yi a kan matashin. Gidado Fari ya shaidawa ‘yan jarida a ranar Laraba cewa Yaro ya amsa laifinsa, tare da bayyanawa jami’an tsaro yadda ya yi wa wasu kananan yara biyar irin wannan danyen aiki.
Fari ya ce wanda ake zargin ya na ikirarin cewa ya na fama da tabin hankali, abin da ba a iya tabbatarwa ba tukuna. Ana zargin shi kadai ne ya ke addabar mutanen kauyen da fyade.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Wanda ake zargi da bata jarirai a Jihar Nasarawa ya shiga hannun Dakarun NSCDC "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?