Tsige sarki Sanusi: Kotu ta mayar da 'yan majalisar dokokin jihar Kano 5 da aka dakatar
Wednesday, 3 June 2020
Comment
ROHOTON: LEGIT.NG
Kotun tarayya ta warware hukuncin majalisar dokokin jihar Kano na dakatar da wasu mambobinta biyar An dakatar da mambobin ne sakamakon kaurewar rikici a zauren majalisar yayin da aka gabatar da kudirin neman tsige Sanusi II
Alkalin kotun, Jastis Lewis Alagoa, ya ce dakatar da 'yan majalisar ya sabawa kundin tsarin mulki Wata kotun tarayya da ke zamanta a jihar Kano ta soke hukuncin dakatar da mambobin majalisar dokokin jihar Kano 5 saboda sun nuna dawa da tsige tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II. A ranar 15 ga watan Maris ne majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da mambobinta guda biyar bisa zarginsu da hannu a sace sandar ikon majalisa yayin sauraren kudirin neman bincike da tsige Sanusi II.
'Yan majalisar da aka dakatar sun hada da; Yau Gwarma mai wakiltar mazabar Kunci da Tsanyawa, Labaran Abdul Madari mai wakiltar mazabar Warawa, Isyaku Ali Danja mai wakiltar mazabar Gezawa. Ragowar sune; Mohammed Bello mai wakiltar mazabar Rimingado da Tofa, da Salisu Ahmed Gwangwazo mai wakiltar mazabar birnin Kano.
Da ya ke zartar da hukunci a ranar Laraba, alkalin kotun, Jastis Lewis Alagoa, ya ce dakatar da 'yan majalisar ya sabawa kundin tsarin mulki.
Alkalin kotun ya bukaci majalisar ta gaggauta janye dakatarwar tare da biyan 'yan majalisar dukkan albashi da alawus dinsu na tsawon lokacin da aka dakatar da su. A ranar 16 ga watan Maris ne aka tsige Sanusi II bisa zarginsa da almudahana duk an samu hargitsi a majalisar dokokin jihar Kano bayan 'yan majalisar biyar sun hada kai tare da kalubalantar kudirin neman a tsige tsohon sarkin.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Tsige sarki Sanusi: Kotu ta mayar da 'yan majalisar dokokin jihar Kano 5 da aka dakatar "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?