--
Tirkashi: Ko kun san cewa ba-hayarku ka iya nuna irin ƙoshin lafiyarku?

Tirkashi: Ko kun san cewa ba-hayarku ka iya nuna irin ƙoshin lafiyarku?



Shin kuna shiga banɗaki domin yin ba-haya ko kuma kashi a-kai-a-kai? Sau nawa ya kamata ku shiga banɗaki a kowacce rana?

Masana sun bayyana mana yadda ya kamata a yi ba-haya dea kuma yadda za ku niya gane irin halin da lafiyarku ke ciki ta hanyar launin ba-hayarku.

Wasu na kalloon yin ba-haya a matsayin wani abin kunya kuma wasu ma ba sa son a san suna yi, amma duk da haka abu ne mai matuƙr mahammanci a rayuwarmu tun da yana taimaka wa jikinmu fitar da sharar da ciki.

Sai dai Chinedum Aranotu, wani likita a Jami'ar Najeriya ta Nsukka, ya ce ya zama wajibi a ƙa yin ba-haya sau ɗaya ko sau biyu a kowacce rana domin tsafatace makasaya.

Ya ce "yin ba-haya sau ɗaya a mako zai iya jawo rashin lafiyar da za a daɗe ana jinya".

Domin fahimtar amfanin tsaftace makasaya a-kai-a-kai, ya kamata a fara sanin mene ne ba-haya ko makasayar kanta.

Mene ne ba-haya?
Ba-haya wata dunƙulalliayar shara ce da ke ƙunshe da sinadaran da ke samu a abinci mai gina jiki da ƙwayar cuta da kuma sauran abubuwan da ba su narke ba, waɗanda ba su da amfani, inda suke fita daga ga jikin mutum.

Wata mujallar lafiya mai suna Healthline ta ce yanayin ba-haya da kuma warinsa sun bambanta tsakanin mutane kuma zai iya nuna alamar ko mai shi yana da lafiya ko kuma a'a.

Sau nawa ya kamata na yi ba-haya a kullum?
Healthline ta ce yanayin lafiyar na'urar narkar da abinci a cikin jiki ne ke tabbatar da ko sau nawa ya kamata a shiga banɗaki.

Shi kuma Dakta Chinedum Aranotu cewa ya yi "duk wanda yake cin abinci kullum ya kamata ya yi kashi kullum saboda rashin yijn hakan ka iya jawo cuta".

Babu takaimamman lokacin da mutum ya kamata ya yi ba-haya, sai dai mujallar Healthline ta ce sau uku a rana zuwa sau uku a sati shi ne daidai. Ita ma mujallar Scandinavian Journal of Gastroenterology ta bayyana haka.

Idan kana ba-haya sau ɗaya a rana, kana da lafiya
Idan kana ba-haya sau biyu a rana, kana da lafiya
Idan kana ba-haya sau ɗaya cikin kwana biyu, akwai matsalar cushewar ciki
Idan kana ba-haya sau ɗaya cikin uku, akwai matsalar cushewar ciki
Kazalika ƙwararru sun yarda cewa yin kashi da safe kafin a ci komai ko a yi wanka ya fi taimakawa lafiyar jiki.

Shi ma Dakta Aranotu ya yarda da wannan bayani amma ya ƙara da cewa "ya kamata mutum ya yi kayansa duk lokacin da ya ji ya matse shi".

Sannan ya ce yin kashi da safe kan taimaka wa jiki karbar abinci mai yawa a rana sannan ya taimaka wurin hana cushewar ciki.

Abin da ke shafar yin ba-haya a-kai-kai

Abinci

Cin wake ko kuma kuma hatsi da ke da sinadadrin fibre da yawa a cikinsa ko kuma 'ya'yan itatuwa, za su taimaka wurin yawan yin ba-haya.

Shan ruwa a-kai-kai da sauran abubuwan sha ma na taimakawa wurin sauƙaƙa makasaya.

Yawan shekaru
Yawan shekaru kan shafi yawan ba-haya saboda yayin da mutane ke ƙra shekaru, makasayarsu na rage yawan motsin da take saba yi. Hanji kan jigata kuma hakan ka iya shafar yawan shiga banɗaki.

Shan wasu ƙwayoyin magani musamman ga tsofaffi.

Motsa jiki

Yawan motsa jiki ka iya taimakawa na'urorin da ke motsa abinci a cikin jiki, ciki har da motsawar makasaya.




KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657



Related Posts

0 Response to "Tirkashi: Ko kun san cewa ba-hayarku ka iya nuna irin ƙoshin lafiyarku?"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?