
Shan kwaya ya karu a kullen COVID-19 —NDLEA
Friday, 26 June 2020
Comment
Yadda mutane ke shan miyagun kwayoyi ya karu sakamakon zaman gidan da aka yi a lokacin dokar kullen COVID-19, a cewar Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Najeriya (NDLEA).
NDLEA ta ce shan kwayoyi ba bisa ka’ida ba ya karu ta yadda masu shan miyagun kwayoyi suka yi ta harhadawa tare da kirkirar kayan maye iri-iri a tsawon lokacin kullen.
Shugaban hukumar, Muhammad Mustapha Abdallah, ya sanar da haka a ganawarsa da ‘yan jarida ta fasashar zamani yayin bikin zagayowar Ranar Yaki da Ta’ammuli da Kwayoyi da Safarar Dan Adam ta Duniya ta shekarar 2020.
Mutum 9,444 ne aka kama da laifukan shan kwayoyi da dangoginsu a Najeriya a 2019. Daga cikinsu kotu ta hukunta 1,195, wasu 795 kuma aka ba su shawarwari, kamar yadda ya bayyana.
“Yananin COVID-19 ya sa masu dogaro da kwayoyi kara shiga hadari domin dama can ba cikakkiyar lafiya garesu ba, al’umma na tsangwamarsu sannan babu halin samun kula da lafiya.
Abin da ya kara tsananta lamarin fiye da komai a yanzu shi ne matsin COVID-19”, inji shi.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Shan kwaya ya karu a kullen COVID-19 —NDLEA"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?