--
Ruwan sama ya yi awon gaba da gidajen 'yan gudun hijira a Borno (Hotuna)

Ruwan sama ya yi awon gaba da gidajen 'yan gudun hijira a Borno (Hotuna)



ROHOTON: LEGIT.NG

Ruwan sama mai matukar karfi ya yi awon gaba da gidajen wucin-gadi na 'yan gudun hijira a Maiduguri  Gidajen na nan a rukunin gidaje masu sauki kudi na Shagari da ke garin Maiduguri a jihar Borno


'Yan gudun hijarar sun yi kira ga hukumomi da su tallafa don gyara musu mazauninsu da ruwan ya kwashe Mamakon ruwan sama ya yi awon gaba da gidajen wucin-gadi na 'yan gudun hijira da ke sansaninsu a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.



Sansanin na nan a Low-cost B Shagari Housing Estate. Akwai gidaje a kalla 40 da aka kafa a sansanin mai zaman kansa tun a shekarar da ta gabata.

Babbar cocin Redeemed Christian Church of God ce ta samar da wadannan gidajen wucin-gadin. Gagarumar guguwar wacce ta fara da yammaci, ta kwashe gidajen tare da kwashe tantin jama'a


Duk da babu wanda ya samu rauni a sansanin 'yan gudun hijirar, amma sun yi kira ga gwamnati da ta gaggauta daukar matakin da ya kamata.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/






KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657



0 Response to "Ruwan sama ya yi awon gaba da gidajen 'yan gudun hijira a Borno (Hotuna) "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?