
PDP ta zargi APC da yi wa lamarin tsaro rikon sakainar kashi
Monday, 15 June 2020
Comment
Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya, PDP, ta sake yin tir gami da Alla-wadai dangane da yadda matsalar rashin tsaro ke ci gaba da tabarbarewa a kasar nan.
Jam'iyyar ta bayyana damuwa matuka dangane da yadda 'yan ta'adda ke zubar da jinin 'yan Najeriya a Katsina, Zamfara, Sakkwato, Borno, Kaduna, Kogi, Taraba da sauran sassa a fadin kasar.
PDP ta ce "tana jin radadin halin tsoro da zalunci da 'yan kasar nan ke fuskanta a hannun 'yan daban daji, masu tayar da kayar baya da kuma masu garkuwa da mutane a sakamakon gazawar gwamnatin APC."
"Gwamnatin APC ta kasa sauke nauyin da rataya a wuyanta, ta gaza inganta tsaro ta hanyar tabbatar da tsare rayuka da dukiyoyin al'umma."
"Babban abin takaici shi ne yadda gwamnatin APC ke ikirarin ta na batar da kudi kan sha'anin tsaro amma kullum lamarin sai ci gaba da tabarbarewa ya ke
“Abinda ya ma fi zama babban takaici shi ne yadda 'yan daban daji ke cin karensu babu babbaka sakamakon gazawar gwamnatin APC da har su ke iya kai hare-hare jihar Katsina da ta kasance mahaifar Shugaban kasa."
"Muna kira ga 'yan Najeriya da su lura cewa, har kawo yanzu gwamnatin APC ta gaza yin bayani kan masu tayar da zaune tsaye da ta shigo da su daga kasashen da ke makwabta da Najeriya musamman Chadi da Jamhuriyyar Nijar domin su hana ruwa gudu yayin babban zabe na 2019."
Jam'iyyar mai adawa ta ce gwamnatin APC ta gaza bijiro da matakai na kawo karshen masu tayar da kayar baya face bayar da sakonnin ta'aziya akai-akai bayan kowane mummunan hari da aka kai kan al'umma. PDP ta janyo hankalin shugaban kasa da ya tashi ya farga "kuma ya farka daga baccinsa domin maido da tsarin ingantaccen tsaro a kasar."
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "PDP ta zargi APC da yi wa lamarin tsaro rikon sakainar kashi "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?