--
Manoma 13 sun mutu sakamakon fita-na-fito da suka yi da yan bindiga a Zamfara

Manoma 13 sun mutu sakamakon fita-na-fito da suka yi da yan bindiga a Zamfara



ROHOTON: LEGIT.NG

A yayin da damina ta fara, manoma na fatan komawa gona amma rashin zaman lafiyan da ke mamaye yankin arewa maso yamma ya tsananta. "Ba mu yi noma a shekarar da ta gabata ba saboda mun fara neman sulhu da wuri. Duk da tsoron da muke yi amma zaman lafiya na dawowa a hankali. "Muna fatan yin noma a wannan shekarar saboda mun fara karbar taki tun cikin watan azumi,

" Jamil, wani manomi a Mayanchi yace. "Sun kawo hari jiya amma mun koresu. A Zaman-Gira, sun fito ta dajin Kontragi. Mun yi kokarin boyewa amma sai suka dawo da safe inda suka kawo mana hari. "Mun rasa mutum 13 daga cikinmu a yanzu. Suna nan a garin Inwallar Gobirawa don har sun kone musu rumbuna. Sun harbeni kusan sau biyar amma basu sameni ba.

"Har yanzu ba mu tabbatar da mutum nawa aka kashe musu ba," Halilu Zaman-Girma wanda ya samu kubuta daga harin ya sanar. Fiye da mutum 300 ne suka tsere inda suka samu mafaka a kusa da Mayanchi sakamakon harin da ake ta kai musu. Wata majiya tace, "Mun yi kokarin fatattakarsu duk da ina da tabbacin mun kashe wasu. Mun ga suna kwashe gawawwaki a kan babura amma ba mu gane yawan wadanda muka kashe musu ba."

Fareed Ibrahim, shugaban Pan African Youth for Social Development, wata kungiyar taimakon kai da kai da ke tallafawa 'yan gudun hijira, ya zanta da jaridar HumAngle a kan hatsarin da ke tattare da kare kai. Ya ce abun takaici shine yadda gwamnati ta zuba wa jama'a ido duk da al'amuran da ke faruwa. Jama'ar yankin sun dogara ne da 'yan sa kai wajen samun kariya.

"A halin yanzu, kariyar rayuka da kadarori sun rataya a wuyan jama'a, wanda hakan na da matukar hatsari. "Sakamakon tsoro da ke cikin zukatan matasa, sun fara shiga kungiyoyin 'yan ta'adda don samun kariya. Kungiyar 'yan sa kai babu yarjewar gwamnati za ta iya tada tarzoma," Ibrahim ya bayyana.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/






KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Manoma 13 sun mutu sakamakon fita-na-fito da suka yi da yan bindiga a Zamfara "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?