--
Kotu ta tsare mutumin da ya yi zina da surukarsa

Kotu ta tsare mutumin da ya yi zina da surukarsa

ROHOTON: LEGIT.NG

Wata kotun gargajiya da ke zamanta a Wuze Zone II ta umurci yan sanda su cigaba da tsare wani Obed Jika da aka ce ya yi zina da surukursa mai shekaru 16. Shugaban kotun, Idayat Akanni ya umurci yan sanda su cigaba da tsare Jika kuma ya dage cigaba da sauraron shariar zuwa ranar 3 ga watan Yuni.

Yan sanda sun gurfanar da Jika mai zaune a Apo a Abuja a kotu bisa zarginsa da aikata laifuka biyu da suka hada da zina da yar uwa ta jini da barazanar cin zarafi.

A baya, mai shigar da kara, Stanley Nwafoaku ya shaidawa kotu cewa wani Mr Dodo Bitrus maaikacin hukumar NSCDC, a Kargarko jihar Kaduna ne ya yi korafi kan lamarin a ofishin yan sanda da ke Apo a Abuja a ranar 21 ga watan Mayu.

Nwafoaku ya ce Jika ya yi zina da yarinyar mai shekaru 16 wacce marainiya ne. Ya cigaba da cewa wanda ake zargin wanda shine ke kula da yarinyar na tsawon shekaru shida da suka wuce ya dade yana zina da ita. Nwafoaku ya kara da cewa wanda ake zargin ya kuma yi barazanar kashe yarinyar idan ta fada wa wani mahaluki abinda ke faruwa tsakaninsu amma ta fada wa yan uwanta da ta tafi ziyara a gida.


Mai shigar da karar ya ce laifin ya saba wa sashi na 390 da 397 na dokar Penal Code. Sai dai wanda ake zargin ya musanta aikata abinda ake tuhumarsa da aikatawa. Mr. Richard Adedoyin, lauyan wanda ake tuhuma ya roki kotu ta bayar da belin wanda ya ke karewa inda ya ambaci sashi na 35(4) and 36(5) na kudin tsarin mulkin 1999.

 Lauyan wanda ake tuhumar ya kuma yi alkawarin wanda ya ke karewa ba zai tsere ba kuma ba zai yi wa wanda ta yi karar barazana ba. Wanda ya shigar da karar ya ki amince da rokon bayar da belin, ya roki kotu ta duba yanayin laifin da ake zargin wadda ya hada da barazana da rayuwar yarinyar.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com



KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/






KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Kotu ta tsare mutumin da ya yi zina da surukarsa"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?