
Kishi kumallon mata: Babbar kawarta ta kasheta akan saurayi
Saturday, 13 June 2020
Comment
Wata sananniyar mai sayar da gashin mata, mai suna Annishair ta mutu bayan ta ci guba a wani abinci da babbar kawarta ta sanya mata.
A yadda rahoton ya bayyana, kawarta din wacce take da wajen sayar da abinci ita ce take aika mata da abinci, inda a hankali ta dinga sanya mata guba a ciki har sai da taga bayanta, akan saurayi.
Budurwar dai ta mutu kwanaki kadan da suka mutu, inda mutane suka dinga tofin Allah tsine akan wannan kawarta da ta zuba mata gubar.
Wata mai amfani da kafar sadarwa na Twitter mai suna Olly ita ce ta wallafa labarin a shafinta, inda ta ce:
“Wata budurwa da take da wurin sayar da abinci, ita ce take aikowa da babbar kawarta da abinci a kowacce rana, inda ta dinga sanya mata guba a ciki, marigayiyar tana sana’ar sayar da gashi ne na mata, inda ta fara sana’ar a watan Janairu. Kawar ta mutu kwanaki kadan da suka wuce. Kuma ta kasheta ne akan saurayi, wannan wace irin rayuwa ce!”
Ita ma wata mai suna Ego Beke cewa tayi: “An sanyawa Annishair guba, mutane basu da imani.”Apparently, this girl who owns a restaurant has been supplying food to and slowly poisoning her friend who owns a hair place since January. The friend died some days ago.— OLLY (@OllyOxx) June 11, 2020
It was over the interest of a man.
What a terrible terrible thing! pic.twitter.com/E5TxXsKLPv
Haka ita ma wata mai suna Swarty a shafin na Twitter cewa ta yi: “Wane irin kishi ne da bacin rai a zuciyar mutum da zai sanya shi ya zubawa amininshi guba a abinci.”annishair was poisoned? Ha people are fucking wicked— ego beke (@luchymoe) June 11, 2020
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.comWhat type of jealousy and anger are you harbouring in your heart that will push you to poison your friend?— SWARTY (@Swartistics1) June 10, 2020
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Kishi kumallon mata: Babbar kawarta ta kasheta akan saurayi"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?