
Kawancen Saudiya A Yemen Sun Kai Hare-Hare Har Sau 450 A Kan Kasar A Makon Da Ya Gabata
Sunday, 21 June 2020
Comment
Gwamnatin kasar Yemen ta bada sanarwan cewa jiragen yakin kawancen Saudia, sun kai hare-hare har sau 450 a kan yankuna daban-daban na kasar a makon da ya gabata kadai.
Kamfanin dillancin labaran Farsnews na kasar Iran ya nakalto Yahyah Saree kakkain ma’aikatar tsaron kasar ta Yemen yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa jiragen yakin kasashen na saudia da kawayenta sun kai hare-haren ne a kan laradunan San’aa, babban birnin kasar da kuma Hajja, Sa’ada, Maarib, Aljauf, Baidaa da kuma Umran.
Gwamnatin kasar saudia tare da goyon bayan kasashen Amurka da sauran kawayenta na kasashen larabawa sun farwa kasar Yemen da yaki ne tun cikin watan Maris na shekara ta 2015 da nufin kifar da gwamnatin kasar da kuma maye gurbinta da wacce tsahon shugaban kasar Abdurabbu Mansur Hadi zai kafa.
Ya zuwa yanzu dai mutane kimani dubu 16 ne suka rasa rayukansu sanadiyar hare-haren na kasashen saudia da kawayenta.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Kawancen Saudiya A Yemen Sun Kai Hare-Hare Har Sau 450 A Kan Kasar A Makon Da Ya Gabata"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?