
Kaico duniya: An kama wani matashi ya na lalata da alade
Tuesday, 23 June 2020
Comment
An gurfanar da Ayokunbi Olaniyi, wani matashi mai shekaru 22, a gaban wata kotun majistare da ke yankin Iyaganku a garin Ibadan, jihar Oyo, bisa zarginsa da saduwa da alade. Rundunar 'yan sanda ta na tuhumar Olaniyi, mazaunin yankin Eleti - Odo a kan titin Iwo a garin Ibadan, bisa tuhumarsa da aikata laifi guda daya;
laifin saduwa da alade, wanda hakan ya sabawa diokar rayuwa ta hankali. Dan sanda mai gabatar da kara, Insifekta Opeyemi Olagunju, ya sanar da kotu cewa an kana Olaniyi ya na saduwa da alade a yankin unguwar Elewi - Odo, Ibadan, da misalin karfe 4:00 na yammacin ranar 2 ga watan Afrilu. Dan sandan ya bayyana cewa Olaniyi ya na aiki da gidan gonar uwargida Adenike Taiwo wanda ke yankin Elewi - Odo a garin Ibadan.
Ya sanar da kotu cewa laifin matashin ya sabawa sashe na 214 (2) na kundin laifuka da hukunce - hukunce wanda aka kirkira a jihar Oyo a shekarar 2000.
Matashin ya amsa laifin da ake tuhumarsa da aikatawa. Mumin Jimoh, lauya mai kare wanda ake tuhuma, ya roki kotun ta kasance mai sassauci a hukuncin da za ta zartar a kan Olaniyi. Lauya Jimoh ya shaidawa kotun cewa mai gonar ta yafewa matashin.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Kaico duniya: An kama wani matashi ya na lalata da alade "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?