--
Hukumar yan sanda ta bukaci kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin kisa kan Maryam Sanda

Hukumar yan sanda ta bukaci kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin kisa kan Maryam Sanda

ROHOTON: LEGIT.NG

Hukumar yan sandan Najeriya ta bukaci kotun daukaka kara da ke zaune a birnin tarayya Abuja ta tabbatar da hukuncin kisa kan Maryam Sanda kan laifin kisan mijinta, Bilyaminu Bello.

Za ku tuna cewa babbar kotun Abuja ta yankewa Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya ranar 27 ga Junairu, 2020 bayan kwashe shekaru biyu ana shari'a.

Jawabin bukatar hukumar yan sanda na kunshe cikin martanin da lauyoyin hukumar sukayi kan bukatar lauyoyin Maryam karkashin jagorancin Joe Kyari Gadzama SAN, ga kotun daukaka kara cewa a soke dokar kisan.

Hukumar ta ce kotun farko ta yi daidai wajen yankewa Sanda hukuncin kisa saboda da gayya ta hallaka mijinta. A cewar lauyan yan sanda,

James Idachaba, Alkali Yusuf Halilu ya yi dai dai wajen duba hujjojin da aka gabatar gabansa kafin ya ta tabbatar Maryam na da laifi kuma ya yanke mata hukunci.

Ya ce idan har kotun daukaka kara ta yafewa Maryan Sanda, toh lallai an baiwa mata daman kashe mazajensu kenan ko da yaushe. Idachaba ya ce an yi doka ne domin ta zama izina ga wasu masu niyyar aikata hakan kuma muddin aka yafe mata,

an kawar da manufar doka kenan. Ya ce tunda an kama Sanda da laifin kashe mijinta, kawai ukubar da ya cancanceta shine kasheta. Ya siffanta kokarin daukaka karan Maryan Sanda matsayin shirme kuma kotu tayi watsi da ita.

A ranar Litinin, 27 ga Junairu, 2020, Jastis Yusuf Halilu ya kama Maryam Sanda da laifin kashe mijinta da wuka. A baya, Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa Sanda ta kashe mijinta a shekarar 2017 bayan wani sabanin da suka samu tsakaninsu. An gurfanar da ita tare da dan 'uwanta, Aliyu Sanda;

mahaifiyarta, Hajiya Maimuna Aliyu, da mai aikin gidanta, Sadiya Aminu, wadanda ake tuhuma da kokarin boye gaskiya ta hanyar

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Hukumar yan sanda ta bukaci kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin kisa kan Maryam Sanda "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?