--
Hotunan yadda titunan Kano suka cika da mutane bayan sassauta dokar kulle

Hotunan yadda titunan Kano suka cika da mutane bayan sassauta dokar kulle



ROHOTON: LEGIT.NG

Duk da sassauta dokar kulle da gwamnatin tarayya ta yi, gwamnatin Jihar Kano ta ce har yanzu dokar kulle tana aiki a jihar a ranakun Litinin, Talata, Alhamis da Asabar. Ta kuma fitar da sabbin kaidoji da dokoki kan yadda za a rika zuwa kasuwanni da wasu wuraren hada-hadan mutane a jihar don rage yiwuwar yada cutar korona.

Kwamishinan watsa labarai na jihar, Muhammad Garba ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito. Sanarwar ta ce bayan tuntubar kwararru a bangaren lafiya da bita kan halin da ake ciki a Kano, an bayar da izinin zirga-zirga da bude wuraren bauta a ranakun Lahadi, Laraba da Juma'a daga karfe 6 na safe zuwa 6 na yamma.

Kasancewar yau 3 ga watan Yuni ya fada a ranar Laraba, Kanawa sun fita kwansu da kwarkwata domin gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

Hotunan da suka fito daga jihar ta Kano ya nuna mafi yawancin mutane ba su kiyaye dokar bayar da tazara ko rashin cudanya yayin gudanar da hidimominsu. Ga dai hotunan wasu kasuwanni da wuraren a Kano kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.




KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com





KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/






KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657


0 Response to "Hotunan yadda titunan Kano suka cika da mutane bayan sassauta dokar kulle"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?