
Hamshakin biloniyan Najeriya ya shirya angwancewa da diyar Trump
Wednesday, 24 June 2020
Comment

Diyar shugaban kasa Donald Trump, Tiffany Trump da saurayinta Michael Boulus dan asalin kasar Lebanoon da Najeriya sun shirya angwancewa sakamakon karfin da soyayyarsu tayi. Masoyan biyu sun saba wallafa kyawawan hotunansu a shafukansu na Instagram, Jaridar The Nation ta ruwaito. A watan Disamban 2019,
Ta hadu da Michael Boulus ne bayan da suka rabu da tsohon saurayinta. Tiffany ta sanar da hakan ne yayin tabbatar da cewa tana soyayya da hamshakin biloniyan Najeriya Michael Boulus. Boulos ya girma a jihar Legas a Najeriya inda danginsa ke da kadarorin biliyoyin daloli. Wannan ne yasa suka dace da diyar shugaban kasar Amurka, Donald Trump.
Masoyan biyu sun fara haduwa ne a kasar Girka inda suka je hutu a watan Yulin 2018. Kamar yadda al'amuran ke nunawa, soyayyarsu kullum kara karfi take yi. Amma kuma, abinda har yanzu ba a sani ba shine, Shugaban kasa Donald Trump ya amince da soyayyar ko bai aminta ba.
An gano cewa Boulus Enterprises ya fara kafa tarihi a jihar Legas bayan da suka fara siyar da kayan karau na mata tare da wasu kananan abubuwan bukata. A wurin 1950, Anthony da Gabriel sun fara fadada kasuwancin inda suka fara shigo da baburan Miele, Durkopp da Goricke. A 1959, sun fara shigo da baburan Suzuki.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Hamshakin biloniyan Najeriya ya shirya angwancewa da diyar Trump"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?