--
Da dumi dumi: Gobara ta tashi a fadar shugaban kasa dake abuja

Da dumi dumi: Gobara ta tashi a fadar shugaban kasa dake abuja



ROHOTON: LEGIT.NG

Kamar yadda mai bai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara a fannin yada labarai ya sanar, gobara ta tashi a Aso Villa  Al'amarin ya faru ne a ranar Alhamis inda wata ma'adanar kayayyaki da ke kusa da majami'ar fadar ta kama da wuta - Gobarar bata ci rai ba don tun kafin zuwan kwararrun masu kashe gobara aka fara kai dauki Gobara ta tashi a fadar shugaban kasa da ke Aso Villa a garin Abuja a ranar Alhamis, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Babban mai bada shawara na musamman ga shugaban kasa a fannin yada labarai, Malam Garba Shehu, ya kwatanta gobarar da karamar gobara. Hadimin shugaban kasar, ya ce al'amarin ya faru a ranar Alhamis inda wata ma'adanar kayayyaki da ke kusa da cocin fadar ta kama da wuta.

Ya ce: "Al'amarin ya faru ne sakamakon wutar lantarki wanda da gaggawa aka kashe tun kafin zuwan masu kashe gobara da ke wajen farfajiyar. "Abun farinciki shine yadda babu wanda ya samu rauni kuma gobarar ba ta zama gagaruma ba."



KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/






KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657


0 Response to "Da dumi dumi: Gobara ta tashi a fadar shugaban kasa dake abuja"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?