--
Fyade: Maza ba katakai bane – Yan majalisa sun bukaci mata su dunga shigar mutuncia

Fyade: Maza ba katakai bane – Yan majalisa sun bukaci mata su dunga shigar mutuncia

ROHOTON: LEGIT.NG

Wasu 'yan majalisa biyu a majalisar wakilai sun bukaci mata a Najeriya da su dinga shigar mutunci don gujewa fyade. Cin zarafin mata da yi musu fyade ya yawaita a kasar nan. A makon da ya gabata ne aka ruwaito yadda aka yi wa wasu mata uku fyade, lamarin da ya kai ga kisan biyu daga ciki. A yayin zaman majalisar wakilan a ranar Alhamis, 4 ga watan Yuni,

Rotinu Agunsoye, dan majalisa mai wakiltar mazabar Kosofe ta jihar Legas, ya mika bukatar hukunta masu yi wa mata fyade a gaban majalisar. A gudumawar da 'yan majalisar suka bada, da yawa daga cikinsu sun bukaci mummunan hukunci wanda ya hada da kisa ko dandaka ga masu keta haddin mata a fadin kasar nan.

A yayin bada gudumawa a kan bukatar, Henry Okon Archibong, dan majalisa mai wakiltar Itu/Ibiono a Akwa Ibom, ya ce yana goyon bayan hukunta masu fyade amma saka dokar kadai ba za ta shawo kan matsalar ba.

Pulse Nigeria ta rahoto ida dan majalisar mai shekaru 53 ya ce za a iya danganta tushen fyade da rashin tarbiyar da ya yawaita a kasar nan.

"Iyayenmu sun Gaza, shugabannin addinai sun gaza, makarantu sun gaza tun daga firamare. "A saboda halin da kasar nan ke ciki, iyaye basu samun lokutan 'ya'yansu. Wannan ne ya kamata ya zama ginshikin tarbiya da horar da maza. "Idan wannan ginshikin bashi da kyau, babu yadda za a yi al'umma ta ginu," yace. Archibong ya ce mata ke janyo maza na musu fyade saboda muguwar shigar fidda tsiraici da suke yi.

Ya ce, "Gaskiya bana goyon bayan yi wa mata fyade amma akwai wata magana da mutane na da ke cewa, idan an bi ta barawo, a bi ta mabi sahu. "Yadda mata ke shigar fidda tsiraici yanzu abun tsoro ce." A majalisar aka ji wata mace ta ce, "za ku iya rufe idanunku" bayan ya kammala jawabi. A jawabin dan majalisa mai wakiltar mazabar Damboa/Gwoza/Chibok ta jihar Borno, Ahmed Jaha ya ce a fara jan hankalin mata su dinga shiga ta gari. "Dole mata su sauya hali wurin yin shiga ta gari don gujewa cin zarafi daga maza. Saboda maza ba itace bane," yace.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/






KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Fyade: Maza ba katakai bane – Yan majalisa sun bukaci mata su dunga shigar mutuncia"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?