FG ta yi barazanar sake rufe masallatai da majami'u
Friday, 5 June 2020
Comment
Gwamnatin tarayya ta yi gargadin cewa za ta sake shawara a kan matakin da ta cimma na bude wuraren ibada a kasar idan har ba a bin sharuddan da ta gindaya. Sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin yaki da korona na shugaban kasa, PTF, Boss Mustapha,
a yayin jawabin kwamitin a ranar Alhamis ya ce an raba wa jihohi sharrudan. Ya ce gwamnatin tarayya na sa ran shugabanin addinai za su amince da sharrudan kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
"Yana da muhimmanci a bi sharrudan domin kaucewa jefa rayukan mutanen cikin hatsarin kamuwa da COVID19. "Muna kira da ayi taka tsan tsan a kowanne lokaci. "PTF za ta cigaba da sa ido kan yadda ake bin sharrudan sassauta dokar kullen da kuma yada cutar ke cigaba da yaduwa.
"Amma ba za muyi kasa a gwiwa ba wurin sauya matakin da muka dauka idan bukatar hakan ta taso domin kare hatsarin yada cutar. "Ya dace a isar da sakon zuwa kananan hukumomi ta yadda za a gano kananan hukumomin da cutar ta yi yawa domin kai musu taimako cikin gaggawa." Ya ce akwai bukatar jihohin su dage wurin wayar da kan mutane game da cutar don hana tsangwama da kawar da canfe canfe,
inda ya kara da cewa sarakuna da shugabannin addinai suna da rawar da ya dace su taka. Mustapha ya shawarci yan Najeriya game da hatsarin da ke tattare da shan magunguna ba tare da tuntubar likitoci ba duk da cewa Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta cigaba da gwajin da ta ke yi na hydroxychloroquine. Sakataren gwamnatin tarayyar ya jadada bukatar da ke akwai na yan Najeriya su rika daukan matakan kare kansu.
A wani labarin kunji cewa gwamnatin jihar Jigawa ta ce za ta saka almajirai 1,322 makarantu bayan an dawo mata da su jihar sakamakon barkewar annobar korona a jihohin kasar nan. Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru ne ya sanar da hakan yayin zantawa da manema labarai a kan annobar korona a ranar Laraba a garin Dutse.
"Kamar yadda na bayyana a jawabi na na baya, an dawowa jihar Jigawa da almajirai 1,322 daga jihohi daban-daban. Mun kula da su kuma muna samar musu da kayayyakin more rayuwa. "Mun mika dukkan almajiran hannun iyayensu banda 23 daga ciki da ke dauke da cutar coronavirus amma suna karbar magani a cibiyar killacewa.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "FG ta yi barazanar sake rufe masallatai da majami'u "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?